Harin Kajuru: Gwamnatin tarayya ta tabbatar da za ta inganta tsaro

Gwamnatin tarayya Najeriya ta tabbatar da cewa, za ta inganta harkokin hukumomin tsaron kasar da kuma tabbatar da an sako da mutum uku da aka yi garkuwa da su a wajen shakatawa a Kajuru da ke jihar Kaduna, ba tare da an raunata su ba. A wata sanarwa da Ministan yada labarai na Najeriya Alhaji […]

Harin Kajuru: Gwamnatin tarayya ta tabbatar da za ta inganta tsaro

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed

Gwamnatin tarayya Najeriya ta tabbatar da cewa, za ta inganta harkokin hukumomin tsaron kasar da kuma tabbatar da an sako da mutum uku da aka yi garkuwa da su a wajen shakatawa a Kajuru da ke jihar Kaduna, ba tare da an raunata su ba.

A wata sanarwa da Ministan yada labarai na Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya fitar a Abuja ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wani dan Najeriya mai suna Mista Matthew Oguche da wata ‘yar Birtaniya mai suna Misis Faye Moone da ‘yan bindigar suka kashe yayin harin da suka wajen shakatawar.