Harin Lassa: Zulum ya tura tawaga ta musamman yankin, an rufe wasu makarantu
Tawagar ta ce gwamnatin jihar na aiki da hukumomin tsaro domin ganin an ceto ɗalibai da malaman da aka sace.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya tura tawaga ta musamman zuwa garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba bayan harin da ’yan ta’adda suka kai makarantar sakandaren gwamnati ta Lassa.
Tawagar ta samu jagorancin Kwamishinan Ilimi, Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-Ƙirƙire, Injiniya Lawan Abba Wakilbe.
- An kashe mutum 10 a wani sabon hari a Binuwai
- Sojoji 2 sun rasu bayan motarsu ta taka bam a Sakkwato
Haka kuma ta haɗa da Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi, Samaila Satumari, Sakatariyar Ma’aikatar Muhalli, Dakta Juliana Bitrus, da sauran manyan jami’an gwamnati.
Da isarsu Lassa, tawagar ta gana da iyayen ɗaliban da abin ya shafa, inda da dama suka nuna damuwa kan makoma da kuma lafiyar ’ya’yansu.
Da yake jawabi ga iyayen ɗaliban, Injiniya Wakilbe, ya miƙa saƙon jajen Gwamna Zulum, tare da tabbatar musu cewa gwamnati na aiki tare da jami’an tsaro domin ganin an ceto ɗaliban da ma’aikatan makarantar da aka sace cikin ƙoshin lafiya.
Ya ce gwamnatin jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai an ceto dukkanin waɗanda aka sace.
Daga nan tawagar ta ziyarci makarantar sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke Lassa, inda aka gudanar da taron gaggawa da shugabannin makarantu, jami’an ilimi, shugabannin ƙaramar hukuma, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Bayan taron, an yanke shawarar rufe makarantu na wucin gadi a garuruwan Dille, Lassa da Chul domin kare rayukan ɗalibai da malamai.
Sai dai ɗaliban da ke zaune domin rubuta jarabawa za a mayar da su makarantar sakandaren gwamnati da ke Uba, domin su ci gaba da karatunsu ba tare da tangarɗa ba.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Askira/Uba, Mada Saidu, ya gabatar wa tawagar jerin sunayen waɗanda harin ya shafa.
Rahoton ya nuna cewa mutum 39 aka sace, ciki har da malamai uku da ɗalibai 36.
Daga cikin ɗaliban 36 da suka ɓace, 25 mata ne, yayin da 11 maza ne.
Tawagar ta kuma kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Uba, Alhaji Aliyu Ibn Samaila Mamza, inda ta bayyana masa matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin magance lamarin.
Tawagar ta yaba wa al’ummar yankin bisa haƙuri da haɗin kai, tare da jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da inganta tsaro a makarantu.