Mutane 87 Boko Haram Ta Kashe a harin Mafa —Mazauna

Za a yi jana’izar mutane 37 da aka gano gawarsu bayan mayaƙan sun yi awon gaba da matasan garin sun ƙona gidaje kimanin 1,000 a rana guda

Mutane 87 Boko Haram Ta Kashe a harin Mafa —Mazauna

Sojoji sun gano gawarwakin mutane 37 da cikin mutane 87 da ake fargabar mayaƙan Boko Haram sun kashe a yankin Kafa na Jiahr Yobe.

A safiyar Talata za a sallar su a Fadar Hakimin Babbangida, bayan a daren Litinin an kai su babban asibitin garin.

Wasu majiyoyi a garin Mafa sun bayyana cewa, “za mu iya faɗa da babbar murya cewa mutane 87 Boko Haram ta kashe.

“Amma za mu iya nuna gawarsu ba saboda wasunsuba cikin daji suka mutu, sakamakon raunukan harbi. Sojoji ba su gano su ba tukuna.”

Mutanen da suka tsallake rijiya da baya a harin sun ce maharan sun ƙone gidaje kimanin 1,000 sannan suka yi awon gaba da matasa masu yawan gaske.

Sun bayyana cewa yawancin waɗanda bin ya yi ajalinsu mata da ƙananan yara da tsofaffi da mata ne, amma ba a kai ga tantance adadinsu ba.

Hakazalika ba a kai ga gano wasu da suka tsere zuwa cikin daji ba, a sakamakon tashin hankalin harin da mayaƙan suka ƙone gine-gine suka wawushe dukiyar mutanen garin.

Ƙazamin harin na ranar Lahadi  ya jefa al’umma Ƙaramar Hukumar Tarmuwa da ma ɗauƙacin Jihar Yobe cikin juyayi sakamakon girman aika-aikan da ’yan ta’addan suka yi.

Aminiya ta samu ganawa da wani mazaunin garin da ya sha da ƙyar, bayan ya samu tserewa zuwa garin Damaturu, fadar jihar, amma ya ƙi amincewa a naɗi muryarsa ko kuma ɗaukar hotonsa.

Ya shaida wa Aminiya cewa ’yan ta’addan sun shigo garin na Mafa ne da wajen karfe 4.30 na La’asar a kan babura sama da 100, kowanne da mutane uku ɗauke da muggan makamai.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa, ’yan ta’addan sun a kan babura kusan 100, sun kashe jama’a, tare da ƙona dukiyoyi masu tarin yawa.

Shi ma wqni mazaunin garin da ya kuɓuta daga harin, Malam Buba Adamu, ya ƙara da cewa waɗanda harin ya rutsa da su akasarinsu  ƙananan yara da matasa da kuma tsofaffi ne haɗe da mata.

Ya ce, “amma a halin yanzu, ba mu san takamaiman adadin mutanen da maharan suka kashe ba.”

A cewarsa, “’yan ta’addar sun yi amfani da bindigogi masu kama da RPG a lokacin harin a Mafa, tare da ƙona ɗaukacin ƙauyen.

“Babu wani abu da ya rage a ƙauyen kusan dukan illahirin ƙauyen yanzu toka ne babu kowa, kusan kashi 80% na mutanen ƙauyen an kashe su har da ƙananan yara.”

Har ila yau, da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho, wani shugaban al’ummar yankin, Lawan Mai Bano, ya ce tun makon da ya gabata ne mayaƙan Boko Haram suka yi barazanar kai hari ƙauyen amma ba su kawo ba sai a wannan karon.

Ya tabbatar da cewa “an kashe mutane da dama, tare da ƙone sama da gidaje 1,000, baya ga shaguna, yayin da ’yan ta’addan kuma suka yi awon gaba da abinci, suka kuma ƙone komai a kauyen.”

Ya kara da cewa “mayaƙan sun buɗe wuta babu ƙaƙƙautawa tare da kashe mutane da dama yayin da wasu mazauna yankin suka tsere zuwa cikin daji.

“Babu wanda ya rage a ƙauyen a halin yanzu da nake magana da ku yanzu; wasu mutane sun bace, wasu an kashe su, wasu kuma sun gudu zuwa daji domin tsira.”

Don haka malamin ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jiha da su kara tura dakaru zuwa ƙauyen domin kare rayukan ’yan kasa domin kauce wa sake afkuwar lamarin.

Bano ya kuma bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da matasa da dama, kafin su banka wa gidaje wuta.

“Ba mu san adadin mutanen da aka sace ba a yanzu,” in ji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce wani mazaunin garin Babagana Goni ya ruwaito cewa wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai farmaki ƙauyen Mafa da yammacin ranar lahadi.

Abdulkarim ya kara da cewa rundunar ba ta kai ga tantance adadin mutanen da maharan suka kashe ba.

Ya kara da cewa, “Ina so in sanar da ku cewa, a yanzu haka an tura jami’anmu da sojoji zuwa ƙauyen domin dawo da zaman lafiya bayan harin.  Muna aiki don samun cikakkun bayanai,” in ji Dungus.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra