Harin Maulidi: Arewa na cikin tasku —Bafarawa
Bafarawa ya bukaci sojoji su biya diyya da kuma sauyin matsuguni ga iyalan da harin Mauludin Tudun Biri ya shafa
Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya bayyana alhininsa kan kisan gilla da jirgin soja ya yi wa wasu Musulmi da ke gudanar da bikin Maulud a Kaduna.
Ya bukaci Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci rundunar soja da ke da alhakin wannan aika-aika da ta gaggauta biyan diyya da sake matsuguni ga wadanda bala’in ya same su da su da iyalansu.
Tsohon gwamnan ya nemi rundunar sojin Najeriya da shugabannin tsaro su yi bincike nan take, don hukunta duk wanda ke da hannu a wannan ganganci don hana aukuwar irin haka a nan gaba.
Bafarawa ya ce, wannan kaskancin da sauran masifun da ke fada wa Arewacin Najeriya sun yi muni, kuma abin tausayi ne ga dukkan mai hankali.
Dahiru Bauchi ya nemi Tinubu ya biya jinin Musulmin da jirgin soji ya kashe a Kaduna
Za mu biya diyyar Harin Mauludin Kaduna —Ministan tsaro
Ya ce “Hakan yana kara nuna bukatar dole a nemi mafita da hada kai a tunkaro lamuran da yankin Arewa yake fuskanta.
“Yana da kyau al’umma da shugabanin a yankin nan dawo bisa hanyar gyara makomar al’umma don kuwa mun shiga cikin tasku da barazana iri daban-daban a kasarmu ta haihuwa.”
Bafarawa ya ce ya yi mamakin ganin duk da wadanan masifun na tashin hankali irinsu Boko Haram, ta’addanci da talauci da yunwa da Arewa ta samu kanta.
“Shin har yanzu wasu daga ketare muke jiran su zo su yi mana gyara ko ceto mu daga wannan matsalolin?”
Ya bayyana rashin mutunta juna, lalacewar tarbiyya, rashin hadin kai, da hassada da nuna halin ko-in-kula da shugabani ke yi musamman dattawa a Arewa a matsayin dalilan yawaitar wadanan matsalolin da kisan gilla da ke fada wa al’ummar yankin.
Bafarawa ya kuma jajanta wa gwamnatin Kaduna, ’yan uwa da iyalan da abin ya shafa.