Harin Maulidi: Yadda muka tsallake rijiya da baya –Mutanen Tudun Biri

Irin bala’in da mutanen kauyen Tudun Biri suka gani a harin dom da jirgin soja ya kai musu, da kuma halin da suke ciki a yanzu, daga bakin wadanda suka tsallake rijiya da baya

Harin Maulidi: Yadda muka tsallake rijiya da baya –Mutanen Tudun Biri

Wasu daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya a kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna sun bayyana yadda Allah Ya kubutar da su daga harin jirgin sama marar matuki da ya yi sanadiyar rasuwar sama da mutum 90.

Sun ce wasu daga cikinsu gawarwakin ma a cikin buhunhuna aka tattara su kafin a binne su a kauyan saboda yadda jikunansu suka tarwatse.

Daya daga cikin mazauna yankin wanda Allah Ya kubutar da shi, Malam Bello Shehu Gara ya bayyana cewa jirgin sama ne ya jefa masu bam har sau biyu suna tsakiyar bikin Maulidi.

“Muna cikin bikin Maulidi ne sai muka hangi jirgin na shawagi a sama kafin mu ankara sai ya sako bam wanda ya halaka mutum kusan 57.

“Sai muka hangi wasu suna neman taimako, mun koma don kai masu dauki sai jirgin ya sake sako wani bam din,” in ji shi.

Ya ce sun binne akalla mutum 74, kafin su kwashe wadanda suka samu rauni 66 zuwa Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna.

Ya ce, “Ba wannan ne karo na farko da muke Maulidi a garin ba da daddare, domin ko a makon jiya mun yi Maulidi kuma babu abin da ya faru sai a wannan karo.”

Shi ma wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Liman ya ce sun binne sama da mutum 90 wasu a cikin buhuna.

Ya ce, “Wani ya rasa matansa biyu da ’ya’yansa, sai jariri ne kawai ya rage.”

An kashe ’yan uwanmu da ’ya’yanmu

Wani matashi dan Tudun Biri, mai suna Idris Dahiru, ya ce a mutum 34 aka kashe a cikin danginsu a harin. “Wannan jirgi (marar matuki) ya kashe al’ummarmu maza da mata da yara, a danginmu mun rasa mutum 34,” in ji Idris.

Ya bayyana cewa a cikin minti 30, jirigin ya jefa musu bam sau biyu.

Wani magidanci, Malam Musa, ya ce kanana yara 12 na gidansu harin ya kashe, ciki har da ’ya’yansa shida, maza uku da mata uku, da kuma ’ya’yan ’yan uwansa shida.

Shi ma wani Kirista da ya rasa ’ya’yansa biyu a harin, Solomon John ya ce ’ya’yansa na cikin Kiristoci uku da aka kashe a harin.

Ya ce ’ya’yan nasa, Kiristoci ne, amma suka halarci taron Mauludin, inda a nan suka gamu da ajalinsu.

Mahaifin wasu yara kanana biyu da suka samu raunuka mai suna Ashiru Ibrahim ya ce kanwarsa mai suna A’isha da ’ya’yanta biyu da kawunsa duk sun rasu a wannan hari.

“Na san mutane da yawa da suka rasu, a yanzu haka ’ya’yana mata biyu Firdausi da Sadiya, na kawo asibiti bayan sun samu raunuka.

Na rasa ’yar uwata A’isha da ’ya’yanta biyu da kawuna,” in ji shi.

Wadanda suka samu raunuka

Ita ma wata dattijuwa mai suna Hauwa’u Yakubu wacce ta samu rauni ita da jikokinta ta ce, “Ban san komai ba sai dai kawai na ji sauka da fashewar abu.”

Wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka da ke kwance a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko sun kasa cewa komai saboda suna cikin rudani.

Ba yanzu muka fara Maulidi ba – Sarki

Sarkin Tudun Biri, Malam Suleiman Shu’aibu ya ce akasarin wadanda suka rasu a harin, yara ne da mata.

Ya ce al’ummar garin sun saba gudanar da tarurrukan Mauludi ba tare da wata matsala ba, sai a wannan karo.

Sarkin kauyen Ifira, daya daga cikin kauyukan da harin ya ritsa da mutanensu a taron, Malam Balarabe Garba, ya yi kira ga gwamnati ta biya diyyar wadanda harin jirign sojin ya shafa.

An kashe mana maza da ’ya’yanmu maza – Matan Kauyen

Matan garin sun koka cewa duk kusan mazan da ke can a kashe su tare da ’ya’yansu maza.

Don haka a cewarsu babu yadda za su ci gaba da zama a yankin kasancewar babu mai kula da su, inda suka bukaci a biya su diyya.

Rahinatu Zubairu cikin hawaye ta ce, “Kanina da wani jaririnsa ne kadai suka tsira a cikin iyalansa 14.”

Ita kuwa A’isha Husaini cewa ta yi mijinta da ’ya’yanta maza biyu sun rasu, sannan cikin ’ya’yan nata akwai mai mace, duk sun rasu an bar ta da karamin yaro.

Sai ta ce, “Wa zai kula da ni a cikin garin nan?”

Ita kuwa A’isha Tundun Biri cewa ta yi ’ya’yanta mata biyu sun rasu a harin.

Akwai bukatar biyan su diyya – JNI, Fityanul Islam

Shugaban Kungiyar Jama’atu Nasril Islam reshen Jihar Kaduna, Farfesa Shafi’u Abdullahi da na Fityanul Islam Sheikh Rabi’u Abdullahi sun bukaci a biya wadanda abin ya shafa diyya.

A cewarsu, akwai bukatar Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki nauyin kula da wadanda aka raunata kamar yadda ta yi alkawari lokacin taron gaggawa da ta kira domin tattauna abin da ya faru a kauyen.

Shi ma Sheikh Rabi’u Abdullahi, Shugaban Fityanul Islam a jihar ya bayyana abin da ya faru a matsayin kaddara daga Allah, amma kuma ya ce akwai bukatar a tallafa musu a asibiti da kuma biyan su diyya.

Dole a biya su diyya – Sheikh Dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya roki Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da an gudanar da cikakken bincike tare da biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe a harin.

Shehin Malamin ya ce, “Muna so Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ta jajirce wajen tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa da aka kashe a wajen bikin Mauludi, tare da hukunta jami’an da suka aikata wannan ta’asa.”

Malamin ya ce, “Muna cikin bakin ciki, yadda mutanen da ke sama suke jefa bam ga wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.

“Laifin wane ne? Laifin gwamnati ne ko laifin wane ne?

“Bai kamata a rika yin wasa da rayukan jama’a ba, mun bukaci a gudanar da cikakken bincike a kan wannan bala’in da ya kashe mutane da dama da ba su ji ba, ba su gani ba,” in ji shi.

Ya ce, “Mun fara tattaunawa da Gwamnatin Tarayya ta hannun Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, ya kuma yi alkawarin cewa za su tabbatar sun yi bincike tare da yin adalci ga wadanda abin ya shafa, idan shugaban ya dawo daga tafiya.”

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, gudanar da cikakken bincike kan jefa bam din da aka ce ba da gangan ba ne, yana da matukar muhimmanci wajen dakile yawan faruwar haka a gaba.

“Domin a baya an kashe wasu Musulmin da ba su ji ba, ba su gani ba a lokacin da suke hanyar komawa gida, an kai musu hari aka kashe su a Jos da kuma hari na baya-bayan nan da suka jefa bam din da ya kashe su, ba za mu amince da haka ba,” in ji shi.

Izala ta yi Allah wadai da kisan

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta Kasa ta yi Allah wadai da kisan da aka yi.

Shugaban Kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya yi kira ga Gwamnantin Tarayya ta yi bincike na gaskiya a kan hakikanin abin da ya faru, kuma ta hukunta masu hannu a cikin wannan lamari.

Sheikh Bala Lau ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu, Ya ba wadanda suka ji rauni lafiya, Ya kuma kiyaye faruwar haka a gaba.

Ba za mu yafe ba – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar ta JIBWIS, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya ce kada gwamnati ta kawo maganar neman a bar wa Allah lamarin, inda ya bukaci a yi bincike sannan a hukunta masu laifin.

Sheikh Jingir ya ce aikin kowane irin shugaba ne ya kare rayukan al’ummar da yake yi wa shugabanci.

Ya kara da cewa, “Tunda Rundunar Sojin Nijeriya ta amince cewa ita ce ta kai wannan hari, hakan ba zai sanya mu ce da niyya aka kawo wannan hari ba?

“Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kafa kwakkwaran kwamitin bincike, wanda zai binciko ainihin abin da ya faru a kan wannan hari da aka kawo.”

 

Ba da gangan ba ne – Sojoji da Gwamnati

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bakin Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya ce kuskure aka samu a yayin da sojoji suka shiga aiki cikin dajin.

A cewarsa, sun yi bakin ciki da ganin abin da ya faru, “Mun gana da shugaban addinai da sarakuna don tattauna abin da ya faru.

“Kuma Kwamandan Rudunar Sojoji ta Daya ya fada wa gwamnati cewa sun shiga aiki ne a cikin daji sai abin ya faru. Muna jajanta wa iyalan da abin ya shafa,” in ji shi.

Har ila yau, Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja a ranar Talata ya ce za a taimaka wa wadanda abin da ya shafa, sannan ya ba da gudunmawar Naira miliyan 10 ga wadanda suka samu a rauni da ke kwance asibiti.

Tinubu ya ba da umarni a yi cikakken bincike

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ba da umarni a yi cikakken bincike kan kisan masu taron Mauludin.

A sakon ta’aziyya, Shugaban Tinubu ya bayyana takaicinsa kan harin, don haka ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike da kuma ba da cikakkiyar kulawa ga wadanda suka samu raunuka a sanadiyyar harin.

Ya yi addu’ar rahamar Allah ga mamatan, sannan ya roki jama’a su kwantar da hankalinsu a yayin da hukumomi ke nazarin abin da ya faru.

Za mu biya diyyar harin Mauludin Kaduna – Ministan Tsaro

Ministan Tsaro, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya sanar sa’o’i kadan bayan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike, cewa Gwamnatin Tarayya za ta biya diyyar wadanda harin ya shafa.

Ministan ya ce Ma’aikatar Tsaro da Gwamnatin Kaduna za su yi aiki tare wajen gudanar da bincike kan abin da ya faru.

Ba da gangan ba ne – Shugaban Sojin Kasa

Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftana-Janar Taoreed Lagbaja, ya ce harin na Tudun Biri ba bisa ganganci rundunar ta kai shi ba.

Ya bayyana haka ne a ranar Talata a yayin ganawa da Shugaban Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Kaduna, Farfesa Shafi’u Abdullahi da sauran masu ruwa-da-tsaki.

Shugaban na JNI ya bayyana fatar sojojin za su dauki matakan da suka dace wajen hana sake faruwar hakan.

Janar Lagbaja, wanda tsohon Kwamandan Rundunar Soji ta Daya da ke Kaduna ne, ya roki Allah Ya yi wa wadanda suka rasu rahama.

Lagbaja ya ce a lokacin da yake aiki a Kaduna, ya jagoranci rundunar yaki da ’yan ta’addar kuma ba a samu irin wannan tsautsayin ba.

Ya kara ba da tabbacin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da aikinta na tabbatar da tsaron kasa.

A hukunta sojojin da suka yi ta’asar, kuma a biya diyya – Dattawan Arewa

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce harin lamari ne mai firgirtarwa kuma dole a dauki mataki.

Daraktan Yada Labarai na NEF, Malam Abdul-Azeez Suleiman, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce dattawan sun bukaci Gwamnatin Jihar Kaduna ta tashi tsaye wajen gudanar da bincike tare da tabbatar da an biya diyya ga wadanda lamarin ya shafa.

“Bayan biyan diyya ga wadanda abin ya shafa, cikakken bincike na da matukar muhimmanci don tabbatar da adalci, tare da hana aukuwar irin haka a nan gaba, da kuma kiyaye ka’idojin kare hakkin dan Adam da dokokin jin kai na kasa-da-kasa.

“Ta hanyar gano musabbabin faruwar lamarin da kuma yanayin da ke tattare da lamarin, binciken zai iya tantance ko wane irin sakaci ne ya faru, tare da hukunta wadanda suke da hannu a lamarin.

“Wannan zai samar da diyya, tare da karfafa amincewa tsakanin sojoji da farar hula,” in ji Suleiman.

Yadda jiragen sojoji suka kashe sama da mutum 400 bisa ‘kuskure’ a shekara 9

Akalla mutum 400 jiragen sojin Nijeriya suka kashe a bisa kuskure daga shekarar 2014 zuwa yanzu.

Daga cikin manyan hareharen da suka fi tayar da hankali, akwai na ranar 17 ga Janairun shekarar 2017, inda sojojin suka kashe akalla mutum 53 a sansanin ’yan gudun hijira na Rann a Jihar Borno.

Akwai kuma wanda aka yi a garin Mutunji da ke Masarautar Dansadau a Karamar Hukumar Maru, inda aka kashe mutum 60 a ranar 17 ga Disamban 2022.

Da wanda aka yi a Jihar Nasarawa, inda aka kashe mutum 40 a ranar 25 ga Janairun bana.

Mutanen da sojojin suka kashe bisa ‘kuskure’ a wurare 16 daban-daban:

  1. Mutum 10 a Jihar Borno a harin ranar 16 ga watan Maris, 2014.
  2. Mutum 58 a Borno 17 ga watan Janairun 2017
  3. Mutum 20 a 28 ga watan Fabrairun 2018
  4. Mutum 11 a Zamfara ranar 11 ga Afrilun 2019
  5.  Mutum 13 a ranar 2 ga Yulin 2019
  6. Mutum 30 a Borno ranar 25 ga Afrilun 2021.
  7. Mutum 9 a Yobe a ranar 26 ga watan Satumbar 2021
  8. Mutum 20 a Borno a ranar 26 ga watan Satumbar 2021.
  9. Mutum 6 a Neja a ranar 20 ga watan Afrilun 2022.
  10. Mutum 12 a Katsina a ranar 6 ga watan Yulin 2022.
  11. Mutum 60 a Zamfara a ranar 17 ga watan Disambar 2022.
  12. Mutum 18 a Neja a ranar 24 ga watan Janairu 2023.
  13. Mutum 40 a Nassarawa ranar 25 ga Janairu
  14.  Mutum 3 a Kaduna a ranar 5 ga watan Maris sin 2023
  15. Mutum 1 a Neja a ranar 18 ga Agustan 2023.
  16. Mutum 90+ a Kaduna a ranar 3 ga Dismabar 2023.

A wani bangaren kuma, matasan Arewa sun nuna fushi, tare da caccakar juna da dattawan yankin bisa yadda suka ce ba a dauki ran dan Arewa a matsayin komai ba.

Wasu sun bayyana yadda kashe wani mawaki dan Kudu ya tayar da hankalin kasar baki daya.

Ana cikin haka ne Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Allah Ya karbi shahadar wadanda jirgin soja ya kashe a Jihar Kaduna.”

Wannan rubutun bai yi wa wasu dadi ba, inda suka rika caccakar sa, har wani mai suna Babangida Muhammad Fagge ya mayar masa da martani cewa, “Amin. Ka ji tsoron Allah ka tuna Ranar Alkiyama Allah zai tashe ka, ka kare kanka.”

Sai dai Aminiya ta gano a daidai lokacin da matasan suke caccakar Kungiyar Dattawan Arewa, kungiyar ta riga ta fitar da sanarwa, inda ta nemi a yi bincike, sannan a biya diyya.

A lokacin da matasan suke maganar dattawa, shi kuma wani mai suna Huzaifa Dokaji ya rubuta cewa, “To wai ku ’yan Arewa, sarakuna masu magana a kan abin da ya shafi rayuwarku a fili kuke so, ko kuma masu ba da shawara a boye?

“Da kun samu mai magana a fili, kun ce sarakuna kurame ya kamata su zama. Saboda haka sai ya daina surutu.

“Da yawan abin da ya kamata din a gaya muku a kan mugunta da zaluncin dan lelen naku, ga shi yanzu kuna kan gani.

“An bar ku da kurame, da ba sa gyara barna a fili, a boye kuma ba ku da tabbas, kuma kuna ta korafin sun ki magana.

“Kuka sani ko Sarkin Musulmi ko na Kano sun kira Tinubu a boye sun yi masa fada, sun ce ba za su yarda ba?

“Ai ku ne kuka ce haka ne dattako da sarauta ko?”

Bambancin ra’ayi

Haka kuma matsalar ta fara rikidewa zuwa bambancin ra’ayin addini, inda aka samu wani mai suna Abu Bilal Assalafiy yana nuna farin cikin kisan da aka yi, inda yake nuna cewa fushin Allah ne ya sauka a kan masu Maulidin, wanda hakan ya kawo musayar yawu a tsakanin bangarori.

Sai dai a daidai lokacin da ake musayar yawun, shugabannin bangarorin Izala da Darika da sauransu duk sun yi Allah wadai da harin tare da kiran a yi adalci.

A kan wannan ne wani mai suna Aliyu Yakubu Yusuf ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Na ga shafin Kungiyar Izala ta Kasa da aka tantance ya yi ta’aziyya kan kisan gillar da aka yi wa ’yan uwa a a Jihar Kaduna.

“Na ga Shugaban Kungiyar Izala na Kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi jimami da ta’aziyya game da wannan kisan kiyashin. Amma fa duk waɗannan ba za a yada su ba.

“Abin da zai yi (ko kuma) ake yadawa shi ne wani wanda ba a sani ba, Abu Bilal Assalafiy wanda ya nuna farin ciki a kan kisan.

“A wajen wasu mutanen, Abu Bilal Assalafiy shi ne wakilin Izala ba wai JIBWIS ta Sheikh Bala Lau ba.

“Bala’i Ya afka wa ’yan uwansu Musulmi, amma maimakon a haɗa kai a nemo mafita, gara a yi amfani da abin a ƙara farraƙa tsakaninmu. Ai shi ke nan mu je zuwa!”