Harin Metele: Boko Haram sun kai wa sojoji hari da jirage marasa matuka
Rundunar sojan Najeriya ta ce, kungiyar Boko Haram ta fara amfani da jirage marasa matuka domin kai farmaki a kan cibiyoyin tsaro na sojojin. Rundunar ta kara da cewa, mayakan Boko Haram su na amfani da fasahar zamani wajen yakar dakarun kasar. A wata sanarwa da Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya fitar a madadin […]
Rundunar sojan Najeriya ta ce, kungiyar Boko Haram ta fara amfani da jirage marasa matuka domin kai farmaki a kan cibiyoyin tsaro na sojojin.
Rundunar ta kara da cewa, mayakan Boko Haram su na amfani da fasahar zamani wajen yakar dakarun kasar.
A wata sanarwa da Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya fitar a madadin hafsan hafsoshin sojan kasa Laftanal Tukur Burutai ta ce kungiyar ta fara amfani da jiragen ne da kuma mayakan wajen kai wa jami’an hari a yankunan Arewa maso Gabas na Najeriya.