Harin Nyanya: An Gaida Sheikh Bala Lau

kasa da mako guda da aukuwar abin takaicin nan na fashewar bom a Nyanya na Abuja, Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa-ikamatis Sunnah (JIBWIS) Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kai ziyarar jaje ga wadanda abin ya rutsa da su a Babban Asibitin kasa na Abuja.Babban Daraktan asibitin, Farfesa BB Shehu wanda Farfesa Jaf Momoh ya […]

Harin Nyanya: An Gaida Sheikh Bala Lau
Harin Nyanya: An Gaida Sheikh Bala Lau

kasa da mako guda da aukuwar abin takaicin nan na fashewar bom a Nyanya na Abuja, Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa-ikamatis Sunnah (JIBWIS) Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kai ziyarar jaje ga wadanda abin ya rutsa da su a Babban Asibitin kasa na Abuja.
Babban Daraktan asibitin, Farfesa BB Shehu wanda Farfesa Jaf Momoh ya wakilta ne ya tarbi shehin malamin, tare da tawagarsa a ofishinsa, kuma aka zagaya da su gadajen da aka kwantar da majinyatar da suka tsira da rayukansu sakamakon wannan wannan babban bala’i.
Masu fashin bakin al’amuran addini a bangaren Arewa sun yaba da wannan ziyara ta Sheikh Bala Lau musamman ganin ita ce ta farko da wata kungiya daga cikin kungiyoyin Musulmi da ke kasar nan ta yi wa wadannan bayin Allah da suka jikkata.
Ko ba komai, a daidai lokacin da wasu baragurbi ke kokarin danganta duk wani aiki na ta’annati da Musulunci da Musulmai, wannan ziyara ta bada wata kafa da wasu cikin masu irin wannan mummunan zato za su sake tunani.
Kazalika ziyarar ta bulloko da kokarin kungiyar Izala a karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau a matsayin kungiya mai fadin kirji, tare da aminta da wadanda ma ba musulmai ba wurin nuna tausayi da jinkai.
“Mun damu matuka yayin da muka samu labarin wannan aiki na ta’annati wanda ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dama tare da jikkata adadi mai yawa.” Sheikh Bala Lau ya shaida wa manema labarai. Ya ci gaba da cewa: “Mun yi Allah wadai da wannan hari saboda babu addinin da yake koyar da wannan mummunan aiki.”
Wani manazarci da yake cikin masu adawa da da’awar kungiyar ta Izala, ya ce: wannan ziyara da jawabi na Sheikh Bala Lau sun kara tabbatar da dacen da kungiyar ta yi a yanzu na shugaba mai ra’ayin jawo kowa a jika, tare da yarda da bambanci. Saboda a cewar manazarcin, majinyatan nan dai ba ’yan Izala ba ne, kai wasun su ma ba musulmai ba ne, amma duk da haka shehin malamin ya kai musu ziyarar jaje da tausayawa tare da ba su gudunmuwar abin da ya sauwaka. Wannan a tunaninsa, ya nuna cewa kungiyar a yanzu ta samu jagoranci mai yalwar kirji.
Musulunci dai dama, ba addini ne na tashin hankali ko hantara ba. Addini na zaman lafiya, kiyaye dokokin zamantakewa tare da tausaya wa ilahirin bani Adama ba tare da la’akari da addininsu ko akidarsu ba. Wannan kuma bai takaita da wata kungiya ta Musulmai ba kadai, a’a, ya hada da duk ilahirin kungiyoyin Musulman ne gaba daya. Saboda dukkansu ba su da wani littafi da ya wuce Alkur’ani, hakazalika ba su da wani abin koyi da ya wuce Manzon Allah (SAW).
Bisa ga dogaro da haka ne ma, Sheikh Bala Lau yake cewa cikin jawabinsa ga manema labarai: “musulunci, addini ne da aka gina shi a kan ginshikin adalci, kyautatawa, gaskiya tare da taimakon mabukata.”
Wannan kam haka yake. Kuma domin hakan ne ma ya sa wannan marubuci ganin dacewar samar da wannan rubutu, don kara yaukaka irin wannan aikin bajinta da Sheikh Bala Lau ya ba da misalinsa, wanda bayan kasancewar aikin a kashin kansa na alheri ne, to kuma akwai wani guzuri da aikin yake tattare da shi, shi ne fadada da’awar Musulunci mai siffanta addinin da son zaman lafiya tare da kuma aminta da mabambantan mutane.
An gaida Sheikh Bala Lau wanda ya hanzarta yin amfani da wannan dama ta ziyara ga majinyatan bom din Nyanya ya isar da sakon Musulunci a aikace, kuma ya sanya rayukan wadanda ba sa kungiyarsa ta Izala daga cikin sauran al’ummar Musulmi numfasawa, saboda ganin dabi’ar yalwar kirji a tare da salon shugabancinsa. Hakika wannan hali abin yabawa ne. Madalla da irin wannan sabon shugaba.
Allah ya yawaita musu irin wannan hali nasa a cikin al’ummar Musulmai.
Madu Iro dan jarida ne kuma manazarci da ke zaune a Abuja
Za a iya samunsa ta 08062216811 ko [email protected]  

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno