Harin Owo: Majalisa ta ba da umarnin kamo maharan
Majalisar Dattawa ta bukaci jami’an tsaro su kara kaimi wajen gano wadanda suka kashe masu ibada a Cocin Katolika na Owo da ke Jihar Ondo. Kimanin mutane 40 ne dai aka kashe, yayin da wasu 80 da suka yi munanan raunuka a harin na ranar 5 ga watan Yuni. ‘Har yanzu harkar kwallon Super Eagles […]
Majalisar Dattawa ta bukaci jami’an tsaro su kara kaimi wajen gano wadanda suka kashe masu ibada a Cocin Katolika na Owo da ke Jihar Ondo.
Kimanin mutane 40 ne dai aka kashe, yayin da wasu 80 da suka yi munanan raunuka a harin na ranar 5 ga watan Yuni.
- ‘Har yanzu harkar kwallon Super Eagles babu armashi’
- An kama matashin da ya kware wajen sayar da gurbataccen bakin mai a Gombe
Majalisar ta kuma bayar da umarnin tura jirage masu saukar ungulu a dazuzzukan yankin domin gano mafakar da`yan bindiga ke kafawa ba bisa ka’ida ba a fadin kasar nan.
Haka kuma ta bukaci jami’an tsaro da rika hada gwiwa idan sun samo rahotannin sirri, domin dakile harin ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya.
Wannan dai ya biyo bayan wani kuduri ne da dan majalisa mai wakilatar Ondo ta Arewa, Sanata Ajayi Boroffice, ya gabatar, inda ya bukaci majalisar ta dauki mataki domin hana lamarin rikidewa zuwa rikicin addini da kabilanci a kasar nan.