Harin Rasha ya hallaka fararen hula 23 a Ukraine
Gwamnan Zaporizhzhia ne ya tabbatar da hakan ranar Juma’a
Rasha ta kai wani harin makami mai linzami wata kasuwar sayar da motoci da ke garin Zaporizhzhia na Ukraine, inda mutum 23 suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata.
Harin makamin ya fada ne kan jerin gwanon motocin farar hula da suka taru don kai agaji ga ‘yan uwa da dangi da ke wani garin da ke hannun Rasha a ranar Juma’a.
- Ukraine da Rasha sun yi musayar fursunoni 300
- Ya kamata duniya ta hukunta Rasha saboda mamaye kasarmu – Zelenskyy
A wata sanarwa da Gwamnan yankin na Zaporizhzhia, Oleksandr Starukh, ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce akalla mutum 28 ne suka jikkata, kuma dukkanninsu fararen hula ne.
Gwamnan ya kuma wallafa hotunan motocin da suka kone, da kuma gawarwakin mutane a kwance a kan titin da aka kai harin.
Wani dan sanda, Sergey Ujryumov, ya ce makami mai linzami samfurin S300 ne aka harba musu, ya kuma samu mutanen da yawa da ke cikin motocinsu, ko kuma suke tsaye a kusa da su.
Sannan ya ce, “Sojojin Rasha da gangan suka kai harin domin suna da masaniyar zuwan fararen hula aikin jin kai”.
Sai dai Vladimir Rogov wani jami’in Rasha da ta nada a Zaporizhzhia, ya dora alhakin harin kan sojojin Ukraine a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Telegram.