Harin Rasha ya jikkata mutum 11 a Kyiv — Zelensky
Rasha ta harba jirage marasa matuƙa sama da 120 da kuma makamai masu linzami 12 cikin dare.
Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce mutum 11, ciki har da yaro ɗaya, sun jikkata sakamakon harin makamai masu linzami da Rasha ta kai kan birnin Kyiv a safiyar Asabar.
A cewarsa, makaman sun afka wa birnin tun kafin a kunna ƙararrawar gargaɗin hare-haren sama.
’Yan jaridar AFP da ke Kyiv sun ce sun ji ƙarar fashewa sau biyu a cikin dare, yayin da ƙararrawar gargaɗi ta fara ƙara ne bayan fashewar farko.
- Sojoji sun yi asarar jami’ai yayin ceto ɗalibai sama da 40 da aka sace a Oyo
- Manchester City ta ɗauki ɗan wasan Leicester Jeremy Monga
A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Zelensky ya ce Rasha ta harba jirage marasa matuƙa sama da 120 da kuma makamai masu linzami 12 cikin dare, inda rabinsu makamai ne ƙirar ballistic.
Ya ce an lalata gine-ginen da suka haɗa da gidaje, ofisoshi da wata makarantar koyar da addini a Kyiv, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da gyaran ɓarna a yankunan Odesa, Sumy, Kharkiv da Chernihiv.
Shugaban Hukumar Mulkin Soja ta Kyiv, Tymur Tkachenko, ya tabbatar da cewa Rasha na kai hari kan babban birnin da makamai masu linzami, inda ya buƙaci mazauna birnin su nemi mafaka.
Zelensky ya ce dakarun kariyar sararin samaniyar Ukraine sun yi nasarar harbo mafi yawan makaman da aka harba, sai dai ba su iya daƙile makamai masu linzamin ba.
Ya sake kira ga ƙawayen Ukraine da su ƙara ba ƙasar tallafin soji, tare da roƙon Amurka ta hanzarta cika alƙawarinta na bai wa Ukraine damar ƙera makaman kariyar sararin samaniya na Patriot.
A cewar mai ba Ministan Tsaron Ukraine shawara, Sergiy Sternenko, idan har makaman sun afka kafin ƙararrawar gargaɗin ta kaɗa, hakan na nuna cewa Rasha ta yi amfani da makamai masu linzami na S-400 wajen kai harin, waɗanda ke da wahalar ganowa ta hanyar na’urorin radar.
AFP ta ruwaito cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ce Ukraine ta kai hare-haren jirage marasa matuƙa kan matatun mai a kudancin Rasha, a wani yunƙuri na kai hari kan cibiyoyin makamashin ƙasar.