Harin Rasha ya yi sanadin mutuwar dalibar Najeriya a Ukraine

Marian da kawarta Fatima na kan hanyarsu na zuwa wajen daukar hoton bikin kammala karatunsu lokacin da bam ya yi bindiga da su.

Harin Rasha ya yi sanadin mutuwar dalibar Najeriya a Ukraine

Wata ‘yar Najeriya mai shekaru 23, Nnani Adaobi Marian, ta rasu bayan ta samu munanan raunuka sakamakon harin sama da Rasha ta kai a birnin Kharkiv na ƙasar Ukraine, kwanaki kaɗan kafin bikin yaye su a matsayin daliban da suka kammala jami’ar.

Marian, wadda ta kammala karatun likitanci a Jami’ar Kharkiv National Medical University, na kan hanyarta ta zuwa ɗaukar hoton murnar kammala karatu tare da kawarta, Fatima Huseynova, a ranar 29 ga watan Yuni lokacin da wani bam ya faɗa yankin Kholodnohirskyi.

Fatima ta rasu nan take, yayin da Marian ta samu munanan raunuka.

An kai ta asibiti sannan daga baya aka tura ta ƙasar Jamus domin ci gaba da jinya, amma daga bisani ta rasu duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi na ceto rayuwarta.

Jami’ar ta bayyana Marian a matsayin ɗaliba mai hazaka, ƙwazo da tausayi, wadda ta fara karatu a makarantar a shekarar 2020.

Ta ce ta yi fice wajen karatu, sannan ta halarci horon aikin likitanci a Jami’ar Cambridge a shekarar 2024 da kuma Jami’ar Biruni a shekarar 2025.

A cikin wata sanarwa, jami’ar ta ce rasuwarta babban rashi ne, tana mai cewa tana shirin murnar kammala karatunta kafin harin ya rutsa da ita.

Harin na daga cikin jerin hare-haren da Rasha ta kai wasu yankunan Ukraine, inda rahotanni suka ce akalla mutum 14 sun mutu, yayin da kusan 100 suka jikkata.

Mutuwar Marian ta sake nuna irin mummunan tasirin da yaƙin Rasha da Ukraine ke yi ga fararen hula.