Harin Silame: Masana sun gargaɗi sojoji kan rashin sanar da gwamnoni

An samu bambancin ra’ayi game da harin da sojoji suka kai Ƙaramar Hukumar Silame a Jihar Sakkwato.

Harin Silame: Masana sun gargaɗi sojoji kan rashin sanar da gwamnoni

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya kai ziyara ta’aziyya ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Silame bayan harin jirgin yaƙin sojoji da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 10, tare da jikkata wasu shida.

Tun da fari sojoji sun kai harin ne bisa zargin ’yan ta’addar Lakurawa ne a yankunan.

A yayin ziyarar, gwamnan ya jajanta wa iyalan mamatan tare da kai musu tallafi.

Gwamnan ya bayyana harin a matsayin kuskure, inda ya bayyana cewa lamarin ya shafi mutanen da ba su ji ba su gani ba, saɓanin abin da aka yi iƙirari.

Sai dai, a martanin rundunar sojin Najeriya, sun ce ba kuskure aka yi ba, suna da tabbaci cewa Lakurawa suka kai farmakin.

Wannan ya jawo cece-kuce da saɓanin fahimta a tsakanin al’umma.

Barista Alkali Sidi, ya bayyana cewa rashin haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da gwamnonin jihohi na kawo cikas ga yaƙi da ta’addanci.

Ya ce dokar ƙasa ta bayyana gwamna a matsayin shugaban tsaro a jiharsa, don haka bai dace a kai hari ba tare da masaniyarsa ba.

“Idan aka samu kuskure aka kashe fararen hula, dole a bi doka don tabbatar da adalci,” in ji Barista Sidi.

Muhammad Nasir, ya yi kira ga gwamnan wajen ganin ya ɗauki mataki a kan lamarin.

“Waɗanda aka kashe fararen hula ne, don haka gwamna ya tabbatar da cewa ba za a bari jininsu ya tafi a banza ba,” in ji shi.

Farfesa Mu’azu Shamaki kuwa, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda sojoji suka musanta kalaman gwamnan.

“Rashin mutunta maganar gwamnanmu raini ne ga al’ummar Sakkwato. Ya kamata gwamnati ta ɗauki lamarin da muhimmanci.”

Harin ya bar al’ummar Sakkwato da tambayoyi game da gaskiyar abin da ya faru, tare da kira a yi adalci don kaucewa sake aukuwar irin wannan lamarin a gaba.