Harin sojin sama ya hallaka mutum sama da 50 a iyakar Borno da Yobe

A yanzu haka dai aka zargin adadin waɗanda suka rasu ya haura mutum 50.

Harin sojin sama ya hallaka mutum sama da 50 a iyakar Borno da Yobe

Aƙalla mutum 56 waɗanda akasarinsu ’yan kasuwa ne, ake zargin sun riga mu gidan gaskiya bayan wani harin jirgin sojin sama da ya auku bisa kuskure a wata kasuwar mako-mako da ke kan iyakar Jihohin Borno da Yobe.

Harin ya faru ne a ranar Asabar a kasuwar Jilli, wadda ke tsakanin Ƙaramar Hukumar Gubio a Jihar Borno da Geidam a Jihar Yobe.

Ana kyautata zaton harin na ɗaya daga cikin ayyukan soji ne da ke nufin kakkabe ’yan ƙungiyar Boko Haram.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin saman na bin sahun wasu da ake zargi mahara ne da suka je kasuwar domin karɓar haraji da kuma sayen kayan abinci, sai dai harin ya yi kuskuren hallaka fararen hula.

Wani ganau ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da tsakar rana lokacin da ake hada-hadar kasuwanci.

Ya bayyana cewa ya ƙirga gawarwaki 56 da kansa, sannan ya taimaka wajen kai wasu da suka jikkata zuwa asibiti.

Aƙalla mutane 14 aka kai Asibitin Ƙwararru da ke Geidam domin kula da su, sai dai ana fargabar adadin waɗanda suka rasu zai iya haura haka.

Wani jami’i a yankin, Malam Lawan Zanna, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa mutane da dama sun jikkata, wasu kuma sun rasu a asibiti, lamarin da ya ƙara yawan waɗanda suka rasu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa kasuwar kan cika maƙil a ranakun da ta ke ci, wanda hakan ya sa asarar rayukan ta yi yawa.

A halin yanzu, magidanta da dama na neman ’yan uwansu da ba su gani ba, yayin da wasu ke jimamin rashin masoyansu.

Mai bai wa Gwamnan Jihar Yobe shawara kan harkokin tsaro, ya tabbatar da faruwar harin, sai dai ya bayyana cewa kasuwar tana cikin yankin Jihar Borno ne.

Ya kuma ba da shawarar a tuntuɓi hukumomin Jihar Borno domin samun ƙarin bayani.

Har zuwa yanzu, Rundunar Sojin Saman Najeriya, ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da lamarin.