Harin sojin sama ya kashe kwamandojin Boko Haram 5 a Borno
An kashe mayaƙan Boko Haram 35 tare da lalata maɓoyarsu da kayan aikinsu.
Wasu hare-hare na Rundunar Sojin Saman Nijeriya sun hallaka manyan kwamandojin Boko Haram biyar a Jihar Borno.
Rundunar ta ce sojojinta masu aiki ƙarƙashin shirin ‘Operation Hadin Kai’ da ke yaƙi da ayyukan masu tayar da ƙayar baya ne suka kashe mayaƙan a hare-hare ta sama da suka kai a ranar 16 ga wannan wata na Agusta.
- ICPC ta kulle asusun Novomed kan badaƙalar magunguna a Kano
- Wani mutum ya rasu sakamakon azumin kwana 19 a Legas
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar, AVM Edward Gabkwet ya fitar a yau Laraba.
Sanarwar ta ce “rundunar ta kai harin ne kan ’yan ta’addan da suka yi hijira zuwa yankin daga wasu wurare da ke kusa.
“Hare-haren sojojin ta sama sun yi nasarar halaka ’yan ta’adda da dama da suka haɗa da manyan kwamandojinsu biyar da kuma yaransu 35 tare da lalata maɓoyarsu da kayan aikinsu.
“Bayanai masu ƙarfi da aka tattara sun nuna cewa manyan ’yan ta’adda da ke wurin da aka kai harin a daidai lokacin sun haɗa da Munzir Arika, Sani Dilla (Dan Hausawan Jubillaram), Ameer Modu, Dan Fulani Fari Fari, da Bakoura Arina Chiki, sai kuma sauran wasu ’yan bindiga 35.”
Sanarwar ta ce, “Ana sa ran nasarar kashe waɗannan kwamandojin da mayaƙansu zai rage ƙarfin waɗannan kungiyoyi ’yan ta’adda na ƙara kai hare-hare ko sake haɗuwa a yankin.”
A ƙarshen watan Yuli, wasu mayaƙa da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kai hari a jihar ta Borno wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 16.