Harin Tudun Biri: Gwamnonin Arewa sun ba da gudummawar N180m
Kungiyar Gwamnonin Arewa ta kuma yi alkawarin kwato hakkin mutanen da kuma ganin sun samu adalci daga hukumomin da ke da alhaki.
Gwamnonin jihohi 19 na Arewacin Najeriya sun ba da gudummawar Naira miliyan 18o domin tallafa wa mutanen da harin jirgin soja ya samu a kauyen Tudun Biri a Jihar Kaduna.
Gwamnonin sun kuma yi shiru na minti daya domin tunawa da mutanen tare da alkawarin kwato hakkokinsu da kuma ganin sun samu adalci daga hukumomin da ke da alhaki.
Shugaban kungiyar gwamnonin, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ne ya sanar da haka a taron da suka gudanar a Kaduna ranar Juma’a.
Gwamnonin sun kuma bukaci hukumomin da ke da alhaki su gudanar da cikakken bincike da nufin hana makamancin harin a nan gaba.
Inuwa Yahaya ya jaddada cewa hakkin gwamnatin ne ta samar da tsaron al’umma, musamman matsalar ta’addanci da garkuwa da mutane da suka addabi Arewa.
Ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan saurin daukar matakin da ta yi bayan harin, amma ya ce ya zama wajibi su hada kai da Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da jama’ar yankin domin tabbatar da tsaron al’umma.
Shi ma gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya jaddada muhimmancin kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga bangaren gwamnati, wanda ya ce ya zama tilas gwamomin ta hada kai wajen tabbtarwa.