Harin Tudun Biri: Sojoji Sun Yi Ganganci —Hedikwakar tsaro
An samu wasu sojoji da hannu dumu-dumu a harin kuma za su fusknaci hukunci
Binciken Rundunar Sojin Najeriya kan harin “kuskuren” da jirgin soja ya kashe kusan mutane 100 a kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna, ya nuna akwai ganganci a cikin harin.
Bayan daukar dogon lokaci tana bincike kan harin rundunar sojin ta ce, jami’an da suka yi wannan aika-aika za su fiskanci hukunci.
Ta ce ta samu wasu jami’an rundunar biyu da hannu dumu-dumu wurin faruwar lamarin, kuma tabbas za su fuskanci kotun soji, domin binciken su ya tabbatar da cewa tun farko bai kamata a saki bama-baman da aka jefa ba.
- Harin Tudun Biri: Gwamnonin Arewa sun ba da gudummawar N180m
- A biya karamin ma’aikaci N615,000 ko a ga bacin rai —NLC
Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro ta Najeriya, Edward Buba, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja ranar Alhamis.
Tun da farko dai rundunar ta dauki alhakin harin, sai dai a wancan lokacin ta danganta lamarin da “kuskure.”
Da yake da karin haske, Edward Buba, ya ce an mika rahoton binciken ga wadanda suka dace, amma ba zai iya bude komai a kan lamarin ba har sai an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotun soji.