Harin ’yan bindiga ya ci mutum 7 har da sojoji a Yobe

Wasu maharan da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kai hari kan matsugunin soja da ke aiki tsaro a karkashin JTF a garin Goniri, karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe inda ya jawo rasuwar maharan hudu da sojoji uku kamar yadda majiyar kusa da jami’an tsaro ta tabbatar. Wata majiya a Goniri ta ce […]

Harin ’yan bindiga ya ci mutum 7 har da sojoji a Yobe
Harin ’yan bindiga ya ci mutum 7 har da sojoji a Yobe

Wasu maharan da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kai hari kan matsugunin soja da ke aiki tsaro a karkashin JTF a garin Goniri, karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe inda ya jawo rasuwar maharan hudu da sojoji uku kamar yadda majiyar kusa da jami’an tsaro ta tabbatar. Wata majiya a Goniri ta ce maharan da yawansu ya kai kusan 200 sun je garin ne a kan babura da motoci a kor-kura kirar Hilud dauke da miyagun makamai da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Asabar inda suka far wa jami’an tsaron aka kwashe sa’o’i hudu ana fafatawa, su kuma al’ummar garin suka rika gudun tsira. Wani jami’in tsaro da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya a Damaturu cewa, ’yan bindigar suna dauke da miyagun makaman da suka dara nasu, kuma da suka ja daga ne, amma da sojojin suka ga harsasansu sun kare, sai suka ja jiki ganin ba su samu dauki daga hedikwatarsu a Damaturu kamar yadda suka nema.Wani mazaunin Goneri da Aminiya ta tattauna da shi a Damaturu bayan ya gudo, ya ce ya ga gawarwakin mutum biyar da gawarwakin sojoji. Kuma wasu gine-ginen gwamnati da suka hada da masaukin baki da cibiyar koyar da sana’o’i an cinna musu wuta. Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin kakakin JTF Kyaftin Eli Lazarus game da harin ya ci tura.