Harin ’yan bindiga ya sa mutane kaura a Zariya

Mazauna unguwannin Zariya na hijira saboda masu garkuwa da mutane sun fitine su.

Harin ’yan bindiga ya sa mutane kaura a Zariya

Masu jaje a kofar gidan Farfesa Aliyu Muhammad Aliyu wanda aka yi garkuwa da shi a kwanakin baya.

Mazauna na ta kaura daga wasu unguwanni a Zariya, Jihar Kaduna saboda yadda masu garku wada mutane suka addabe su.

Akalla unguwanni 10 ne suka bayyana fargabarsu saboda ayyukan ’yan bindiga, wanda hakan ya sa da dama daga cikinsu tashi zuwa wasu wuraren.

“Mutane da dama sun bar unguwarmu wadanda suka ci gaba da zama kuma na cikin zullumi saboda al’amarin kara tabarbarewa yake yi,” inji wani mazuwanin Unguwar Kuregu mai suna Kennethi Chinanuife.

’Yan bindiga sun kai wani hari a unguwar Kuregu-Wusasa inda suka bindige wani soja da wani farar hula bayan sun yi musayar wuta da jami’an tsaro inda suka kona wata motar soja suka kuma yi garkuwa da wasu mutum shida a kusa da Bakin Dogo.

Malam Musa Shehu, mazaunin unguwar Tsallaken Dogo ya ce tun bayan harin dan mai shekara bakwai ke cikin matsananciyar damuwa, yake kuma matsa masa da tambaya, yaushe za su bar unguwar?

Masu jaje a kofar gidan Farfesa Aliyu Muhammad Aliyu wanda aka yi garkuwa da shi a kwanakin baya.

Malam Shehu, wanda ke ci gaba da zama a unguwar bayan wasu makwabtansa sun yi hijira saboda rashin tsaro, ya ce yana cikin tashin hankali game da abin da zai iya samun iyalansa.

Sai dai kuma ba shi da wani wurin da zai koma saboda bai san inda zai koma ba.

“Dana na yawan tamabaya ta: ‘Baba yaushe za mu tashi?’ Amma sai in ce masa ya yi hakuri saboda nan ne gidanmu, ni ma a nan aka haife ni. Babu inda za mu iya zuwa, saboda hakan yanzu mun shiga rokon Allah Ya kawo mana agaji,” inji shi.

Harin na ranar 25 ga Disamba, 2020 ya auku ne mako guda bayan ’yan bindiga sun kai hari a gidan Shugaban Sashen Nazarin Samar da Hatsi na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi, Farfesa Aliyu Muhammad a Zariya, suka yi garkuwa da shi sannan suka kashe dansa Abdulaziz.

A makon jiya kuma kadai an yi garkuwa da mutum biyu da suka hada da wani likita da wani jami’in tsaro a Zariya.

Mazauna sun kadu da yadda masu garkuwa da mutane suka fitini Zariya mai manyan ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da suka hada da Jami’ar Ahmadu Bello, Kwalejin Tukin Jirgin Sama, Makarantar Yaran Sojoji, Makarantar Horon Kuratan Sojoji, da sauransu.

A baya dai Zariya ta kasance cikin aminci duk da ayyukan ’yan bindiga da suka addabi kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari da ke makwabtaka da ita.

Sai dai daga watan Nuwamban 2020 ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka addabi yankin inda suke satar jiki su shiga garin cikin dare su sace mutane don neman kudin fansa.

Manyan garkuwa da mutane da aka yi

Akalla manyan mutane uku ne aka sace a Zariya daga watan Nuwamban 2020 daga manyan makarantu.

A Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Nuhu Bamalli, ’yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Sashen Injiniyan Kwamfuta, Bello Atiku da ’ya’yan makwabcinsa biyu a ranar 14 ga Nuwamba, 2020, suka sake su bayan kwana tara bayan an biya kudin fansa.

Awanni kadan bayan sakin su kuma ’yan bindiga suka kutsa gidan wani malami a cikin Jami’ar ABU, Ibrahim Bako suka yi garkuwa da shi da matarsa da ’yarsa.

A hanyar tafiya da su ne ’yan sanda suka yi musayar wuta da ’yan bindigar har maharan suka saki matar da ’yar, shi kuma suka tafi da shi.

Ba su sake shi ba sai da ya yi wata guda a hannunsu aka kuma biya kudin fansa sama dan Naira miliyan biyu.

Ana cikin jimami karuwar garkuwa da mutanen ne kuma ’yan bindiga suka kai hari gidan Farfesa Aliyu Muhammad da ke unguwar Wusasa a ranar 17 ga watan Janairun 2021.

’Yan bindigar sun kashe dansa daya suka jikkata wani, shi kuma mahaifin suke ci gaba da neman miliyan N10 a matsayin kudin fansarsa.

Kawo yanzu, iyalan Farfesa Aliyu sun ce maharan ba su suko shi ba, amma dansa, Dokta Khalifa Aliyu ya ce suna da kyakkyawar fata cewa za a cimma matsaya da maharan su sako shi.

Sai dai bai yi karin bayani game da tattaunawar biyan kundin fansar ba saboda dalilan tsaro.

Mazauna na kaura daga gidajensu

Akalla unguwanni 10 ne ke cikin zullumi saboda ayyukan ’yan bindiga, wanda ya sa da dama daga cikinsu yin kaura

Unguwannin sun hada da Kuregu, Wusasa, Dala, Madachi, Tsallaken Dogo, Sayen Mai Doya, Dorayi, Buzai, Kofar Gayan, da Anguwar Kaya.

Yawancin unguwannin da matsalar ta fi addaba na wajen garin Zariya ne kuma gidajensu a warwatse suke.

Wani mazaunin Kuregu mai suna Kenneth Chinanuife, ya shaida wa wakilinmu cewa ya yi kaura daga unguwar ne bayan an yi garkuwa da dan uwansa.

Kenneth ya ce ya yi ta samun sakonnin barazanar za a yi garkuwa da shi, wanda hakan ya sa shi yin kaura daga unguwar.

Yawancin mutane sun tashi daga Kuregu “wadanda suka ci gaba da zama kuma na cikin zullumi saboda al’amarin kara tabarbarewa yake yi,” inji shi.

Wani mazaunin Madachi ya ce an yi garkuwa da matarsa mai ciki da ’yar uwarta a bara, kuma masu garkuwar sun kusa harbe kaninsa a lokacin da ya yi yunkurin tserewa.

“Tun daga lokacin unguwar ta fita a raina, duk da cewa gidan nawa ne,” inji shi.

Wani mai gida a Madachi mai suna Adamu ya ce yawancin masu gidaje a unguwar na so su sayar su koma wasu unguwanni amma babu masu sha’awar sayen gida a unguwar.

“Unguwarmu na kan mahadar zuwa kauyen Galadima na Karamar Hukumar Giwa, hakan ya sa ’yan bindiga ke samun saukin kai mana hari,” inji shi.

Adamu ya bayyana damuwa kan yadda garkuwa da mutane ke kara yawaita.

Ya ce Madachi da ke kafin layin dogo da kuma Galadima da ke kafin gadar da ta hade Wusasa da Kuregu sun zama tarkon mutuwa saboda ’yan bindiga na yawan bi ta nan su kai hare-hare.

Mai Unguwar Kuregu-Wusasa, Alhaji Ahmadu Amfani ya bayyana takaicinsa bisa yawaitar hare-haren da ya ce sun fara yaduwa har a Zariya.

Ya ce, “Duk da wadannan matsalolin, muna rokon mutanenmu kar su tashi,” ya kara da cewa an fara wayar da kan mazauna kan hanyoyin kare kawunansu da iyalansu.

Wani dan banga a yankin ya yi kira ga takwarorinsa da kar su yi kasa a gwiwa saboda tabarbarewar yanayin tsaro a yankin, inda ya jaddada muhimmancin su nuna kishi wurin kare unguwanninsu daga mamayar ’yan bindiga.

“Galibin wadanda ake kamawa suna yi wa ’yan bindiga leken asiri sakin su ake yi; Mu kuma da muka sadaukar da kawunanmu don kare al’ummarmu, rayuwarmu na cikin hadari saboda ana sako su, sai su yi ta kawo mana farmaki,” inji shi.

Mun tuntubi kakakin rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige domin mu ji ta bakinsa game da halin da ake ciki game da sha’anin tsaro a Zariya.

Sai dai an shafe awanni bai amsa kira-kirayen da da muka yi ta masa ta waya ba har muka kammala hada wannan rahoton.