Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

Gwamnan ya buƙaci jami’an tsaro da su tabbatar an gano waɗanda suka kai harin.

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda suka jikkata a harin da ’yan bindiga suka kai kasuwar Ngalda da ke Ƙaramar Hukumar Fika.

A ranar Litinin da yamma, wasu ’yan bindiga suka shiga kasuwar, suka kashe mutane takwas, tare da jikkata wasu 11, sannan suka yi awon gaba da Naira miliyan 16.

Gwamnan, ya bayyana baƙin cikinsa game da al’amarin, sannan ya bayar da umarnin a gaggauta tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa.

Bugu da ƙari, ya umarci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike don gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da tabbatar da cewa an hukunta su yadda ya dace.

“Dole ne ku gano dalilin wannan lamari, sannan ku tabbatar da an ɗauki matakan da za su hana irin haka a nan gaba,” in ji Gwamna Buni.

Kasuwar Ngalda ita ce babbar kasuwar dabbobi a yankin, inda ’yan kasuwa daga jihohin maƙwabta ke zuwa domin hada-hadar kasuwanci.

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya