Harin ’yan tawayen Houthi ya kashe sojojin gwamnati 14 a Yemen

Tun shekara ta 2015 ne ’yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran ke yaƙi da gwamnatin Yemen.

Harin ’yan tawayen Houthi ya kashe sojojin gwamnati 14 a Yemen

Aƙalla sojojin gwamnatin Yemen 14 ne suka mutu bayan wani hari da ’yan tawayen Houthi suka kai a kudancin birnin tashar ruwa na Hodeidah, kamar yadda wani jami’in sojin gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da ita ya shaida wa AFP a ranar Lahadi.

Jami’in ya ce dakarun gwamnati sun yi nasarar dakile harin da aka kai a gundumar Hays, da ke kudancin Hodeidah, bayan artabu da ya ɗauki sa’o’i da dama tun daga wayewar garin ranar Asabar.

Ya ƙara da cewa an samu mace-mace da jikkata a ɓangaren mayaƙan Houthi, sai dai bai bayyana adadin waɗanda aka kashe ko suka jikkata ba.

Tun shekara ta 2015 ne ’yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran ke yaƙi da gwamnatin Yemen a rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da jefa ƙasar cikin ɗaya daga cikin mafi munin matsalolin jin ƙai a duniya.

A halin yanzu, mayaƙan Houthi na iko da babban birnin ƙasar, Sanaa, da kuma mafi yawan yankunan arewacin Yemen, ciki har da Hodeidah da ke gabar Tekun Bahar Maliya, yayin da gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da ita ke iko da mafi yawan yankunan kudancin ƙasar.

Ko da yake an samu tsagaita wuta da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shiga tsakani aka cimma a shekarar 2022, rikicin tsakanin ɓangarorin biyu bai ƙare gaba ɗaya ba.

A ranar Juma’a ce mayaƙan Houthi suka yi barazanar kai hare-hare kan filayen jiragen sama da wasu muhimman kadarori na Saudiyya, wadda ke ɗaya daga cikin manyan masu goyon bayan gwamnatin Yemen da ke Aden.

Ƙungiyar ’yan tawayen ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan zargin cewa Saudiyya ta hana wani jirgin saman Iran sauka a Yemen.