Harkar fim ta kai ni inda ban zata ba — Adaman Kamaye

Gaskiya sha’awa ce ta shigo da ni harkar fim.

Harkar fim ta kai ni inda ban zata ba — Adaman Kamaye

Adaman Kamaye

Zahara’u Sale Pantami wadda aka fi sani da Adaman Kamaye a fim din Dadin kowa na tashar Arewa24 ta bayyana yadda ta fara fim da burinta na gaba a hirarta da Aminiya.

Wace ce Adaman Kamaye?

Sunana Zahara’u Sale Pantami wacce aka fi sani da Adaman Kamaye a tashar Arewa24. An haife ni a garin Gombe.

Na yi rayuwa a Gombe. Na girma a Gombe, yanzu kuma rayuwa ta dawo da ni Kano, da yake dama Kano garin kakannina ne, wato ’yan asalin wani gari da ake kira Garko.

Yaushe kika tsunduma harkar fim?

Gaskiya sha’awa ce ta shigo da ni harkar fim. Ina ganin finafinan Hausa ina sha’awa har Allah Ya kawo lokaci, aka zo kaina, har na fara kuma ga shi ana tare da ni.

Wasu ’yan fim sukan ce da wasan dabe suka fara. Ke ta ina kika fara?

Ai tun ina tare da su nake sha’awa, amma ban yi fim ba saboda a lokacin ni na fi sha’awar in tafi Makka.

Muna tare da su Tsigai su Biba Problem, Allah ji kan rai da su Kara-da-Kiyashi duk muna tare.

Sai bayan na je Saudiyya na gama zaman Saudiyya, na dawo sannan na fara harkar fim shekara 19 ke nan.

Daga cikin finafinan da kika yi wanne za a ce ya fito da ke?

Fim din Dadin Kowa na tashar Arewa24 wanda nake fitowa a Adaman Kamaye.

Sunanki Zahara’u amma Adaman Kamaye ya danne wancan sunan ko me ya sa hakan?

Sunan rawar da nake takawa ke nan a fim din da ake kallo sosai, domin Zahara’u ma ya bata da Adaman Kamaye ake kirana.

Ana ganin kamar Adaman Kamaye ba ta da kirki, a fim ne kawai ko kuwa?

Adama kam ba ta da kirki, amma a shirin Dadin Kowa. Ba ta da hali gaskiya saboda irin wannan halin da take nunawa shi ya sa mijin bai jin dadi.

Wato ana nuna duk mace mai hali irin na Adaman Kamaye ta gyara halin da take yi domin ba abu ne mai kyau ba.

Me za ki ce a kan yadda aka faro harkar fim zuwa yanzu da ake samun sauyi na zamani?

An samun ci gaba sosai tunda an samu sauyin zamani da tsare-tsaren sauyin zamani kamar yadda ka fada.

Ka ga da haka ake daukar mu yanzu, ka ga sai an bi matakin duk da ya dace ake daukar mu, idan za a dauki mutum a harkar fim.

Duba da irin halayyar Adaman Kamaye a fim, yaya kike fuskantar mutanen gari a zahiri idan kun hadu?

Gaskiya ina fuskantar tsangwama wani lokacin. Akwai wani dattijo da ya yi min tsawa har duka ya so ya kawo min sai da na kauce.

Haka wani na shiga gidan mai zan sha mai, shi kuma ya shigo a kan babur, to yana gabana sai na ce to idan kun zuba ku ba ni a kan hanya nake.

Yana ta kallo na bai gane ni ba, yana ta kallo na kamar ni kamar ba ni ba. Da ya ji na yi magana kawai sai ya ce ‘la matsiyaciya’, ya ce min tsinanniya.

Sai na ce masa ai wasa ne ba haka halina yake ba. Sai ya ce to don me ya sa ba za ki ce ba za ki yi ba?

Fada fa da gaske da tsohon mutane shi ne abin da na gani wanda ba zan manta ba.

Yadda kike magana a fim haka muryarki take a zahiri?

Ba halitta ba ce, larura na samu idan za ka dubi finafinaina na baya ba haka muryata take ba, na samu matsala a makogwarona, wanda Hajara Usman ta dauke ni, ita ta kai ni asibiti ba zan taba mantawa ba.

Da aka yi min aiki, sai likitan ya ce to in daina shan sanyi da sauransu kuma in daina magana da karfi.

Daga baya aka samu matsalar kiyaye wasu dokokin, sai aikin ya warware aka sake mayar da ni wajensa dama kuma mutum ne mai saurin fushi sai da aka ba shi hakuri sannan ya sake duba ni.

Yaya batun kalubalen da kika fuskanta?

Na samu tsangwama gaskiya tun daga cikin gidanmu, tunda ni dai da wayona na shiga cikin harkar nan.

Kuma ban sam ba sa so, kamar Isa Ali Pantami wanda shi ne dan autan su babana kusan in ce har yanzu ba ma jituwa sosai saboda wannan harkar. Haka na yi ta ba su hakuri.

Yaya kuke da Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami?

Baba ne a wurina, shi ne dan autan su babana.

Yaya batun nasarori fa?

Ba su da adadi wallahi saboda akwai inda ban isa in taka ba, amma ta dalilin fim na taka.

Shawararki ga masu kaunarki?

Shawarata ga masoyana baki daya na fadin duniya idan sun ga mun yi kuskure don Allah a sanar da mu ta hanyar da ta dace, domin mu gyara. Sannan ina rikon alfarma su rika yi mana uzuri.

Wadanda muke kawaye da su a Facebook da Twitter da sauransu idan suka tura mana sako ba mu bude ba, sai ka ji ana cewa ai wance ta cika wulakanci ko wane ya cika wulakanci, to ba haka ba ne wallahi idan dambu ya yi yawa ne ba ya jin mai.

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara