Harkar gwangwan ce ta daga ni – Yusha’u Ruba
Alhaji Yusha’u Alhassan Ruba, shi ne Shugaban Masu Sayar da Kayan Gwangwan na Jahar Jigawa, mutun ne da ya yi gwagwarmaya a bangaren kasuwanci daban-daban a Jihohin Filato da Jigawa a fagen saye da sayarwa a fadin Najeriya. Haka kuma Alhaji Yusha’u ya shahara a fagen harkar gwangwan da harkar motocin hawa, kuma har gobe […]
Alhaji Yusha’u Alhassan Ruba, shi ne Shugaban Masu Sayar da Kayan Gwangwan na Jahar Jigawa, mutun ne da ya yi gwagwarmaya a bangaren kasuwanci daban-daban a Jihohin Filato da Jigawa a fagen saye da sayarwa a fadin Najeriya. Haka kuma Alhaji Yusha’u ya shahara a fagen harkar gwangwan da harkar motocin hawa, kuma har gobe yana alfahari da sana’ar gwangwan saboda yadda ta rufa masa asiri. Wakilimmu ya sami zantawa da Alhaji Yusha’u Alhassan Ruba a cibiyarsa da yake saya rda kayan gwangwan dake Sabuwar Kasuwar Dutse. A cikin wannan tattaunawa da ya yi da wakilimmu Umar Akilu Majeri, dan kasuwan ya tabo batun irin gudunmawar da ya bayar a jahohin Jigawa da Filato, wajen inganta rayuwar matasa ta hanyar gwada masu sana’ar gwangwan da sauran sana’o’in hannu da zai bai wa matasan damar tsayawa da kafafunsu. Ruba ya ce yana cikin wannan sana’a ce tun zamanin mulkin Janar Buhari na soja, lamarin da ya ce ya sami damar bude wuraren koyawa matasa sana’a da dama a Jahar Jigawa tun daga masu sayar da kwali da masu sayan leda da kuma masu sayar da gwangwanin karafa, babura da motoci da kuma harkar gwanjon motoci da gwamnati ke yi a duk lokacin da za ta yi. Ga dai yadda yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:
Rankai dade ka gabatar mana da kanka a takaice.
Sunana Alhaji Yusha’u Alhassan Ruba, ni haifaffen Ruba ne a karamar Hukumar Kafin Hausa dake nan Jahar Jigawa, amma na girma ne a Jos babban birnin Jahar Filato kuma na fara gwagwarmayar rayuwa ne a nan Filato wato Jos yau fiye da shekara 25, tun zamanin mulkin Janar Buhari na soja, wadda a lokacin Yohana Madaki shi ne Gwamnan Filato na soja. A lokacin da na fara kasuwanci na fara ne da sana’ar sayar da manja a bakin kofar rumfar yayana, Malam Yahaya Alhassan a Kasuwar Laranto, da sana’a ta yi karfi sai yayana ya bar min shagonsa na ci gaba da dauko manja diro-diro da man kuli ina sayarwa. Kafin na sauya sana’a na kai ga mallakar yara wadanda suke taimaka min a fagen saye da sayarwa har mutum biyar, wasu suka dauki nauyin sayo manja wasu kuma su ne suke zuwa Kano su sayo mana man kuli a wajen Alhaji Haruna, yayin da masu manja suke zuwa Kalaba su sayo.
Da na yi karfi ne na kafa yarana a wajen na koma gefe na fara sayar da kayan gwanjo na sawa adai wannan kasuwar ta Laranto, kuma har ta kai ni ne nake zuwa Kwatano ko Kasuwar Malabil wata kasuwace a tsakanin Kwatano da Nijar, inda na mallaki shagunan sayar da gwanjo guda uku, daya a Filin Ball na Jos da kuma daya a New Market daya kuma a Nasarawa Jos. Yanzu haka Alhaji Usman Kunya shi ne Sakataren ’Yan Gwanjo na Jos kuma ya na daya daga cikin yarana da na kafa a harkar gwanjo a can Jahar Filato. Daga nan da na ga tafiya ta fara yin nisa shi ne na koma sayo motoci ina sayrwa, wato motocin Tokumbo daga Kwatano ina gyara wa ina kaiwa Fatakwal ina sayarwa.
Daga nana me ya faru kuma hark a tsunduma wannan harka?
Daga nan sai kara hadawa da kawo Babura daga Legas zuwa Arewa, kuma ta kai sai da na zama dila (dealer) na sayar da babura a Jos, har zuwa lokacin da Abacha ya kafa dokar shigo wa da Babura sababbi ne muka daina shigo su. To akwai wani mutun wadda ake cewa Mamman Dan Sambo, shi ne ya saka ni a harkar sayar da tsofaffin motoci, muna gyara wa muna sayar wa a karkashin ofishin Alhaji Yahaya Kofa Motors wadda yake kan Titin Bauci Road 18A, saboda muna kusa da inda ‘yan gwangwan suke. Daga nan ne fa na sami damar fadawa kasuwar ’yan gwangwan, inda na sami sanin sirrin kasuwar gwangwan a Jahar Filato inda na girma.
Ita kasuwar ta gwangwan a ina ta ke?
Ita ta na Jos ne a gidan Alhaji Adamu Dikos, shi ne na yi saboda ‘yan gwangwan manya na fara sayowa da manyan karafa wajen gwamnati ina sayar wa har ta kai na bude ofishina na farko a karamar Hukumar Lantan a Jahar ta Filato kuma na dauki wani yaro acan Lantan dan kabilarsu na ba shi Manaja, lamarin da ya sa ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya na kauyen Lantan suka amshi bakuncina da girma, saboda irin cigaban da na kawo masu a yankin.
Ya ya aka yi ka dawo gida Jahar Jigawa?
Na dawo gida ne Jahar Jigawa saboda kishi, saboda yanzu jahar take tashe, kuma jahar ta na bukatar mutane irinmmu wadanda suka san harkar wadanda za su taimakawa matasa su sami ikon dogaro da kansu, saboda ba komai ne za a ce gwamnati za a dogara da ita ba, musamman a wannan karni da rayuwa ta yi tsauri, ayyuka ba sa samuwa, sannan nau yi ya yi wa gwamnati yawa, tunanin hakan ya sa na dawo gida domin ni ma na bada tawa gudunmawar wajen ciyar da Jahar Jigawa gaba.
Tun yaushe kenan ka dawo Jigawa?
Na dawo Jigawa lokacin mulkin Sule Lamido, amma fa da ma ina zuwa ina komawa ne, lokacin mulkin Saminu Turaki amma ganin yadda Gwamna Lamido ya dora jahar akan tafarki madaidaici, ya sa na kwaso duk iyalaina da duk harkokina na dawo Jahar Jigawa da burin na bada duk tawa gudunmawa wajen taimaka wa jahar ta kara bunkasa musamman a harkar kasuwanci.
Me ka yi daka dawo gida. Ina nufin ta ina ka fara ?
Da na dawo gida na fara da bude cibiyar ‘yan gwangwan anan bayan gidan Rediyon Freedom, ni na kafa wannan cibiyar kuma na bude ofishina a gidan Alhaji Amadu Kwayamawa, kuma anan ne nake tara duk kayan gwangwan da na sayo daga duk wata karamar hukuma dake fadin jahar kafin a fitar da kayan zuwa inda za a sayar. Haka zalika yanzu haka ina sayar da motoci a kofar gidan Alhaji Mahammadu Mai Fulani Dutse cikin alfarmarsa, da ma na gaya maka ina yin sana’ar sayar da motoci tun ina Jos, haka zalika ina yin sana’ar waya, domin ita waya karamar harka ce, amma sana’ace mai rufin asiri matuka gaya, duk inda ka same ni ina sayar da waya kuma ina sayanta domin inci riba.
A wajan batun harkar sayar da wayar hannu kuma, yanzu haka na koyawa yara harkar waya sama da mutun goma, kuma ina tare da da su, haka zalika a wajen harkar gwangwan na gwada wa yara sama da 30, amma saboda yanzu matasan yanzu rayuwarsu wata irice suna san kudi ne da gaggawa, da yawa ba su tsaya sun koyi sana’ar ba, da dama sun gudu sun kasa tsayawa, na yi kokarin saka yaran kauyanmu amma fa da dama ba su iya tsayawa sun koyi sana’ar ba.
Wacce sana’ace ta fi saurin kawo kudi daga cikin sana’o’in da ka lissafa?
Daga cikin sana’oin da suka fi kawo min kudi, babu kamar sana’ar gwanjon motoci da gwamnati take mana, domin ita sana’a ce ta manyan karafa, daga ita sai gwangwan, domin ita gwangwan sana’a ce mai sirri sosa,i baka sanin sirrinta sai ka shiga cikinta.
Kenan da su ka yi gida da mota da iyali?
Sana’ar gwangwan ce da gwanjon manyan karafa ita ce ta rufa min asiri na kai ga mallakar gidana na kaina a garin Jos a tsakiyar birnin kuma ina da abin hawa da yara takwas, kodayake mu a wajenmu duk mai sayar da mota ba ya cewa yana da mota, domin komai tsadar mota idan dai a wajenmu ne, to ta sayarwa ce, mu ba ma ajiye mota a matsayin ta muce ta hawa, domin komai namu na sayarwa ne.