Harkar Noma Ce Kaɗai Za Ta Samar Da Zaman Lafiya A Najeriya — Peter Obi

A duniya Najeriya ce kasar da ta fi yawan gonakin da ba a nomawa, kuma abin mamaki da yawansu a Arewacin Najeriya su ke.

Harkar Noma Ce Kaɗai Za Ta Samar Da Zaman Lafiya A Najeriya — Peter Obi

Peter Obi

Dan Takarar Shugabancin Najeriya na Jam’iyyar LP a Zaben 2023 ya bayyana cewa riƙo da harkar noma ce kaɗai hanyar magance rashin tsaro, yunwa, fatara da talauci a Najeriya.

Obi ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Birnin Kebbi yayin ci gaba da zagayen buɗa baki da ya ke yi a jihohin Najeriya.

Ya ce, “a duniya Najeriya ce kasar da ta fi yawan gonakin da ba a nomawa, kuma abin mamaki da yawansu a Arewacin Najeriya su ke.”

Obi ya ce da za a maida hankali kan noma to da an yi sallama da matsalar tsaro da talauci a Najeriya.

Ya kara da cewa “zuwansa Kebbi ya ciyar da masu azumi ɗari, ya kuma ƙaddamar da rijiyar burtsatsai mai amfani da hasken rana a Hutawa wani kauyen Fulani a Birnin Kebbi.”

Da ya ke jawabi ga Peter Obi, Gwamnan Jihar Kebbi da Sakatarensa Alhaji Yakubu Bala-Tafida ya wakilta ya ce, “gaskiya ne abin da Obi ya faɗi, shi yasa suka fara saka dan ba wurin tallafin noma ga al’ummar jihar”.

Tafida ya kuma yi godiya ga tsohon Gwamnan na Jihar Anambra kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

Ya ƙara da cewa, gwamnatinsu ta sayi taki na Naira Biliyan 2.9 ta raba wa al’ummar jihar, ba tare da la’akari da jam’iyyar da mutum ya fito ba.

Haka zalika, ya ce “mun samar da injinan ban ruwa da sauran kayayyakin aikin gona ga dubban mutane a Jihar.”

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce, babban makasudin da ya sa take wannan yunƙuri shi ne su saukaka wa manoma hanyar aikinsu.

Ya ƙara da cewa, hakan zai taimaka wajen samar da abinci mai rahusa ga jama’ar jihar.