Harkar noma na cikin mawuyacin hali -Farfesa Dadari

Farfesa Salihu Adamu Dadari malami ne a Cibiyar binciken aikin gona ta Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana matsalolin da suke damun harkokin noma a Nijeriya da hanyoyin da za a bi a warware wadannan matsaloli. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Aminiya: A matsayinka na masani […]

Harkar noma na cikin mawuyacin hali -Farfesa Dadari

Farfesa Salihu Adamu Dadari malami ne a Cibiyar binciken aikin gona ta Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana matsalolin da suke damun harkokin noma a Nijeriya da hanyoyin da za a bi a warware wadannan matsaloli. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: A matsayinka na masani kan harkokin noma yaya kake ganin yadda harkokin aikin noma yake tafiya a kasar nan a halin yanzu?

Farfesa Dadari: Babu shakka akwai matsaloli da dama da suke damun harkokin noma a kasar nan. Matsala ta farko da take damun harkokin noma a Nijeriya ita ce, gwamnati tana taimaka wa manoma a tsare-tsaren da take shiryawa amma kuma wannan taimako da gwamnati take yi wa manoma akwai kulunboto a ciki, domin manoma ba sa gani a kasa. Ya kamata a tallafa wa manoma, a tanadar masu da kasuwa mai inganci da nagarta domin su samu su rika sayar da kayayyakin da suka noma.
To, amma a tsare-tsaren da gwamnati take yi na tallafa wa manoma akwai siyasa a ciki, don haka abubuwan ba sa isa ga manoman. Ko a kasashen Amerika da Burtaniya da suka shahara suna tallafawa manoma, domin idan manoma suka noma abinci ya wadata a wadannan kasashe farashin kayayyakin amfanin gona ya fadi, gwamnatocin wadannan kasashe suna da runbunan adana kayayyakin amfanin gona, sai su tallafa wa manoman ta hanyar saye kayayyakin amfanin gonar su adana. Abin da ya kamata gwamnatin Nijeriya ta rika yi ke nan. Ta karfafa wa manoma gwiwa domin su rika noma wadatattun kayayyakin amfanin gona wadanda za a rika fitar da su zuwa kasashen waje, kamar Nijar da jamhoriyar Benin da Mali, da dai sauransu. Amma gwamnatin Nijeriya ba ta iya yin haka, saboda haka duk maganar da gwamnatin Nijeriya take yi kan tallafa wa manoma a halin yanzu magana ce ta siyasa.
Kamar a lokacin jamhoriya ta biyu gwamnati ta wadata manoma da taki a kasar nan. Domin a lokacin manomi zai je sito ya sayi taki ya bayar da kudinsa ya dauka ya tafi gona abinsa. Amma a yanzu idan gwamnati ta kawo taki sai ta raba wa ‘yan siyasa. Don haka a yanzu noma yana cikin wani mawuyacin hali a Nijeriya.
Aminiya: To wadanne hanyoyi ne kake ganin za a bi a warware wadannan matsaloli da suke damun manoma?
Farfesa Dadari: Hanya ta farko ita ce a daina cusa siyasa a harkokin tallafa wa manoma. A nuna wa manoma cewa gwamnati ta san da zamansu kuma za ta taimaka musu tsakani da Allah. Kuma a inganta hanyoyin da manoma za su bi su rika sayar da kayayyakin amfanin gonar da suka noma a cikin sauki. A dawo da cibiyoyin sayen kayayyakin amfanin gona na gwamnati da ake da su a da, irin su Marketing board, kuma a rika bada farashi mai kyau.
Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta fahimci cewa al’ummar Nijeriya sama da miliyan 100 sun dogara da aikin noma ne. Domin baya ga manoman, akwai masu kasuwancin kayayyakin amfanin gonar da masu sarrafa kayayyakin amfanin gona a kamfanoni da masu dakon kayayyakin amfanin gona, da dai sauransu. Saboda haka ya zama wajibi gwamnati ta inganta harkokin noma a Nijeriya domin shi ne rayuwarmu. Don haka a samar da hanyoyi masu kyau da kasuwanni ingantattu na noma,a rika kai kayayyakin amfanin gona ana sayarwa da daraja. A bude masana’antu masu sarrafa kayayyakin amfanin gona.
Yanzu idan ka lura Kamar su tumatur da mangoro da gwaiba da sauransu,lalacewa suke yi a kasar nan, saboda babu yadda za a yi da su. Amma idan aka sarrafa su za a rika fitar da su zuwa kasashen waje ana sayarwa. Mun yi sa’a Allah ya yi mana albarka a Nijeriya, domin kusan dukkan wani kayayyakin amfanin gona da itatuwa idan ka shuka shi a Nijeriya zai yi. Don haka Allah Ya yi mana gata a Nijeriya.
Idan muka rungumi noma a Nijeriya kowa zai samu aikin yi, domin a aikin noma ga leburori masu aiki a gona, ga masu shuka, ga masu noma, ga masu zuba taki, ga masu girbi, ga masu bugu da dinki da daukar buhuna, ga masu dauka su kai kasuwa, ga masu sayen kayan amfanin gonar su kai kamfanoni, ga masu aiki a kamfanonin da suke sarrafa kayan amfanin gonar, da dai sauransu.
Babbar illarmu a Nijeriya ita ce rashin shugabanci na gari. Domin muna da shugabanci na bukulu da yaudara da zalunci da cuta da ba a tausaya wa talakawa. Idan ka lura, a shekarar da ta gabata ma gwamnati ta shigo da masara daga kasashen waje. Alhalin masarar ta lalace, domin ta yi shekaru a ajiye.
Aminiya: Wane tasiri ne kake ganin noma zai yi wajen bunkasa tattalin arzikin Nijeriya?
Farfesa Dadari: Tasirin yana da yawa, na ba ka misali da kasar Amurka da Birtaniya, duk rigimar da suke yi a kasashen duniya ba su soma ba sai da suka tabbatar da cewa suna da abincin da za su ci na sama da shekaru 10 a ajiye. Kaga kamar kasar a China duk da cewa sune suka fi kowa yawa a duniya, amma suna da abinci wadatatce. Kamar mu a Nijeriya za mu iya noma shinkafar da za mu ciyar da kasashen Afrika gaba daya. Ai a da da noma muka dogara a Nijeriya, domin da noma aka gina matatun man kasar nan. Saboda haka ina kira ga gwamnatocin Arewa da al’ummar Arewa su hada kai su yi wa noma adalci.