Harkar sayar da fara na fuskantar matsala a Kano

daya daga cikin sana’ar da ke ba mutane da yawa abin yi a Kano shi ne sayar da fara. Akwai akalla mutane sama da dubu shida wadanda suka yi rajista da kungiyar masu sai da fara don yin wannan sana’ar. Sana’a ce wacce sama da shekara goma sha biyar ake yinta. Duk da cewa ba […]

Harkar sayar da fara na fuskantar matsala a Kano

daya daga cikin sana’ar da ke ba mutane da yawa abin yi a Kano shi ne sayar da fara. Akwai akalla mutane sama da dubu shida wadanda suka yi rajista da kungiyar masu sai da fara don yin wannan sana’ar. Sana’a ce wacce sama da shekara goma sha biyar ake yinta. Duk da cewa ba a samun fara a Kano, masu kasuwancin sukan tafi jihohin Yobe da Bauchi don saro farar sannan su kuma su kasa don sayarwa.
Da yake bayanin yadda suke gudanar da kasuwancin farar, Sakataren kungiyar  Masu sayar da fara ta kasa reshen jihar Kano, Malam Sharu Ghazali, ya ce kasuwancin fara abu ne da ake yinsa lokacin sanyi kawai, “Ita fara ba a samu ta sai a lokacin sanyi, shi ya sa kasuwancinta ma sai a lokacin sanyi. Mukan tafi jihar Bauchi da Yobe don mu saro farar kuma idan muka kawo sai mu raba wa ‘yan kungiyarmu don su sayar,” in ji shi.
Ghazali ya kara da cewa, da Naira dubu goma sha uku mutum na iya fara kasuwancin fara, domin buhu yakan kama daga Naira dubu goma zuwa sha ukun. Yanayin kasuwa ma ba laifi, inji shi, domin mutane na sayen farar, ko don su kai gidajensu a ci ko kuma don su soya su sayar.
Da yake bayanin yadda ake kama farar, sakataren ya ce masu kamawa sukan fita daji da dare lokacin sanyi zuwa wurin da faran sukan taru suna makale da juna don sanyi. Wannan sanyi shi yake sa a kama su da sauki,domin ba su iya tashi sama, “Mu kanmu kafin mu je inda ake kama farar muna mamakin yadda ake kama su buhu-buhu, amma da muka je inda suke kamawa sai muka ga ashe fita suke yi da dare suna daure da toci a goshinsu suna bin farar, inda suke kwance akan juna don tsanananin sanyi. Kawai damka daya ake yi sai ka ga mutum ya cika hannunsa da fari masu yawa,” inji Ghazali.
Ya ce a lokaci guda sukan je su sayo kamar buhu hamsin don su raba shi, kuma kwano daya na fara yakan kama daga Naira dari uku da hamsin zuwa dari hudu.
Bayan an kama farar akan bi wadansu hanyoyin sarrafa su kafin a kai kasuwa, “Da farko idan aka kama farar, a kan zuba a cikin buhu a daure, sai a jefa buhun cikin tafasasshen ruwan zafi don ya bararraka, bayan nan sai a shanya su su bushe, sannan a sake mai da shi cikin buhu a dinke, sai a kai kasuwa.”
Sarrafawar ba a nan ta tsaya ba, bayan an kawo kasuwa, mai saye kuma idan ya saya, yakan je gida ya sa mata dan mai sai ya soya ta, bayan an dan sa masa yaji da magi. ‘Yan mata masu kasuwancin fara sukan daure a leda suna sayarwa Naira goma-goma. Don karin armashi ma, sukan cire cinyoyin da fukafukan su daure su daban don masu bukata.
Da yake karin haske a kan harkar tasu, shugaban kungiyar, Malam Salisu dahiru, wanda ya samu wakilcin Malam Magaji Tahir, ya ce sun yi kyakkyawan tsari don gudanar da sana’arsu yadda bata-gari ba za su shiga ciki ba, “Da farko dole sai mutum ya zo wurinmu ya yi rajista kafin ya fara sana’ar sayar da fara kuma ba za mu yi masa regista ba sai mun bincika mun ga cewa ba shi da wata matsala.”
Ya kara da cewa, farfagandar da wadansu kan yi cewa da wani irin sinadarin  kashe kwari ake amfani wurin kama farar duk karya ce, domin sai da suka je har inda ake kama farar suka ga yadda ake kamawa kuma suka je inda ake sarrafa shi, kuma a duk wuraren babu inda suka ga an yi amfani da wani magani, “Wannan farar muna kaiwa gidajenmu muna ci da iyalinmu kuma a matsayi mu na ‘yan jihar Kano ba za mu sayo abin da zai cutar da mu sannan mu kai wa iyalanmu su ci ko mu kawo wa mutanen jiharmu su ci don su cutu ba.
Wannan zargin da ake musu ne ya sanya kasuwancin tasu ta kan dan samu tsaiko, domin a kan tsoratar da masu saye a ce akwai guba a ciki.
Ya kara da cewa, ita fara a likitance ma tana da amfani, domin kamar zuma take, duk bishiyar da ta sauka a kai ta ci, to akwai magani a cikin bishiyar.
Da take bayanin amfanin fara a jikin dan Adam, wata malamar asibiti a asibitin Abdullahi Wase na Nasarawa, wacce ta kware a fannin abinci, wadda ta nemi a sakaye sunarta, ta ce, fara na daga cikin nau’in abinci mai gina jiki (protein) kuma bayan haka tana taimakawa wajen motsa hanji don ta kasayar da duk abin da jiki ba ya bukata, watau da turanci (roughage)