Harsashin Da Aka Harbe Ni Na Nan A Cikina —Fasinjan Jirgin Kasa
“Likitan ya yi amfani da rigata domin tsai da jinin da ke zuba har zuwa gwiwata, sannan ya yi amfani da safar hannu ta aikinsu ya lalubo harsashen da kuma almakashi amma bai yi nasara ba,” in ji shi.
Daya daga cikin fasinjojin jirgin kasa da ’yan tadda suka sako a ranar Litinin bayan garkuwa da su ya bayyana cewa har yanzu harsashin da aka harbe shi na jikinsa.
Sidi Sharif, wanda ya tsallake rijiya da baya ya bayyana hakan ne a ofishin Tukur Mamu, wani dan jarida wanda ya shiga tsakani har aka sako fasinjojin a ranar Litinin.
- ’Yan Arewa 170 Da Muka Kama Ba ’Yan Ta’adda Ba Ne —Amotekun
- Haramta yin acaba zai kawo karuwar ta’addanci —Masu babura
“A lokacin da muke tsaka da tafiya a jirgin da ’yan ta’adda suka kawo hari suna ta harbe-habe… da muna tsare a hannunsu an harbe ni ciki, wani likita ya yi kokarin a cire min harshin amma hakan bai yiwu ba.
“Likitan ya yi amfani da rigata domin tsai da jinin da ke zuba har zuwa gwiwata, sannan ya yi amfani da safar hannu ta aikinsu ya lalubo harsashen da kuma almakashi amma bai yi nasara ba,” in ji shi.
Sharif bayan ya yi godiya ga Allah da kubutowar su, ya ce a yanzu zai je asibiti ne a dauki hoton cikinsa don gano inda harsashin ya makale.