Harshen Hausa ke gaban kowane harshe a Afirika – Farfesa Ibrahim Mukoshy

Wane ne Ibrahim Mukoshy?A to, ni kam na yi karatu, na yi aiki kuma na yi ritaya, yanzu kuma ina ci gaba da aiki a matsayin kwantaragi a Jami’ar Usman danfodiyo.Kamar yadda aikinka ya kasance yi wa harsuna, musamman na Hausa hidima, ko ta yaya haka ta faro?Na yi hidima amma dai ni ban zabi […]

Harshen Hausa ke gaban kowane harshe a Afirika – Farfesa Ibrahim Mukoshy

Wane ne Ibrahim Mukoshy?
A to, ni kam na yi karatu, na yi aiki kuma na yi ritaya, yanzu kuma ina ci gaba da aiki a matsayin kwantaragi a Jami’ar Usman danfodiyo.
Kamar yadda aikinka ya kasance yi wa harsuna, musamman na Hausa hidima, ko ta yaya haka ta faro?
Na yi hidima amma dai ni ban zabi wannan ba na bar wancan, duk tare muke tafiya da su duka. Na yi aiki a kan Hausa, na yi aiki a kan Fulatanci kuma na yi aiki a kan Larabci. Haka nake tafiya tare da su, ban zabi guda ba, na ce wanga ya fi wanga ba; kowane harshe yana da irin ta shi ranar kuma yana da irin na shi amfani ga irin na shi mutane. Na yi aiki a wurare daban-daban. Na karantar da Hausa da Fulatanci a Amurka. Na karantar da Hausa, kamar kuma yadda na yi wa Fulatanci aiki a Jami’ar Bayero Kano. Na yi aiki a tsangayar koyar da Harsunan Najeriya a Jami’ar Usman danfodiyo Sakkwato; wadansu aikace-aikacen kanana, na yi su ne a irinsu Zariya ko Maiduguri da sauransu. Wadansu ayyukan na harshe ne gaba daya, wato abin da ya shafi harshe ba wai harshen wane ba. Haka har na kai fagen yin ritaya kuma yanzu an kirawo ni ina taimakawa.
A tsawon wadannan shekaru da ka dauka kana wannan hidima, wadanne kalubale ka fuskanta?
Ana tambayar cewa wane kalubale mutum ya fuskanta, a duk abin da mutum ya sa gaba, kana aiki a kansa, wadansu abubuwa ba kalubale ne ba. Sai dai ba ka iyawa ka dauka ko kuma ka fara ka kasa amma ba kalubale ne ba. Kana aikinka, ko dai ka iya ka yi yadda ya kamata, ko kuma kana tsakar yi wani abu ya gitta maka ya hana ka yi, ko don ya fi karfinka ko don ka kasa. Amma babu batun kalubale, babu mai kalubantarka ga aikin da kake son yi. Babu mai cewa wane kada ka yi aiki kaza.
Za mu so mu san ’yan misalan irin wadannan kalubale ko abubuwan da suka faru a yayin gudanar da aikinka.
Yawancinsu dai, idan wajen karatu ne za ka ce kana son samun digiri, idan ka samu ka iyar ka samu, falillahil hamdu. Wani bi kuma za ka fara ka zo ka samu wadansu abubuwan ka kasa, ka yar ka kama wani abun. To ban samu haduwa da irin wadannan ba. Na shiga makaranta, na yi karatu, na gama digiri na daya, na gama digiri na biyu kuma na gama digirin-digirgir. Mai yiwuwa ne duk wani kalubale da zan samu, rayuwar ce ke son haka. Misali na fara da neman digiri na uku a Amurka, sai na ga cewa akwai wani dan abu a tsakanina da malaman, tsakanina da rayuwar, tsaknina da wasu abubuwa haka; na ce kai na yafe amma daga karshe na je na kammala.
Idan muka zo ga karan kansa shi hareshen Hausa, wanda ya zama abin da za a kira sha kwaranniya; a matsayinka wanda ya dade yana harka da shi, me za ka ce game da shi?
Harshen Hausa yana daya daga cikin manya-manyan harsuna na Afirika. A bisa gaskiya, cikin duk harsunan Afirika, ya fi kowane aiki da cikawa. Domin Bahaushe ne kadai ke zaunawa ya yi magana a kan siyasa, shi kadainke zaunawa ya yi magana a kan tattalin arziki; shi kadai ke zaunawa ya yi magana a kan zamantakewa kuma shi kadai ke zaunawa ya yi magana a kan sana’o’i da kimiyyar da fasahar duka. Amma duk sauran harsunan suna kokarinsu amma wadansu ayyukan ba su iya daukar su, domin ba su da kayan aiki. Ko ita kanta Hausar da ta girma kuma ta kasaita, akwai wadansu ayyukan idan an ba ta su, kauce musu za ta yi, domin ba ta da abin yin wannan aikin. Amma dai ana nan ana kokarin a ga an kai.
An dade ana ta kwadayin kiran cewa ya dace kasa kamar Najeriya ta samar da wani harshe na gida ko wasu harasa domin su zama na hukuma. Wasu ma na ganin cewa harshen Hausa ne ya kamata a dora wa wannan aiki, me kake ganin ya kawo wa harshen cikas domin samun wannan martabar?
Ba shi da wani abu da ya hana shi zama haka nan, domin gwamnati ta bayar da damar a yi haka nan. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dade tana son ganin an zabi harshe domin zama na hukuma. Na san na shiga wasu taruka da dama, ba ma Hausar nake wakilta ba, ina wakiltar Fulatanci ne, ina daya daga cikin wadanda suka tsaya tare da Hausawa. Amma idan an zo wajen taron Hausa, abu guda ne; Najeriya ta taba zaben harsuna guda tara ta ce ku zabar mani guda ko biyu ko uku a cikin su tara. Aka zo, da Bare-bari da Fulani suka mara wa Hausa baya, ka ga ka samu uku? Sauran shidan nan ba su so. Me za ka ce wa gwamnati? Ba ka iyawa, domin duk sai Najeriya ta yarda, ta bunkasa, ta tashi daga barcin da take yi, ta gane cewa dole tana bukatar kasarta. Idan ta kai wannan fage, ba a ma bukatar taro. Wani kawai zai zo ya ce, kai daga yau a yi Hausa ko kuma daga yau a yi Yoruba ko kuma daga yau a yi Ibo; domin su ne harsunan Najeriya manya guda uku. Yoruba dai ana yin Yarabanci a Najeriya, ana yi a kasar Benin; Hausa ta bazu ko’ina. Akwai ta a Najeriya, a Nijar, don duk Bahaushen da ka gani, kodai daga Najeriya yake ko kuma daga Nijar. Sannan akwai burbushinta a Ghana, inda duk Hausawa suka je fatauci, idan sun zauna sun kafa kasuwa, nana ma za ka iske akwai ta. Akwai Hausa daga nan har Senegal, za ka iske duk inda Hausawa suka zauna, akwai kuma ’yan kasar sun iya Hausa. Idan ka duba wajen arewaci, Makka, Sudan, Libya, Moroko, duk inda ka je za ka iske Hausawa suna zaune a ciki. Na ga Bahaushe har da Bafillace a kasar Afirka ta Tsakiya kuma sun tafi can sun zauna, sun yin kaka-gida. Wato yaduwa kam Hausa tana yaduwa, sannan bayan yaduwar kuma duniya ta yarda cewa Hausa wani abu ne, domin kafafen watsa labarai da ke aiki da Hausa suna da yawa. Ingila, Amurka, Jamus, Faransa, Masar, Iran, China duk suna da sashin Hausa a gidajen rediyonsu, wato abin yana da yawa. Saboda haka Hausa ma ta fi karfin Bahaushe, wasu ke da ita.
Ga shim un gan ka a kasar Nijar domin taron tunawa da marigayi Farfesa Muhammad Hambali Jinju. Kun yi aiki tare da shi, shin wane irin mutum ne shi?
Wallahi mutum ne mai hakuri, don kuwa kowane mutum mai hakuri in tura ta kai bango yana walkatowa. Mutum ne shi wanda bai yarda da abin da bai da tushe ba. Duk abin da bai da tushe, ko an shekara dubu ana fada masa, shi kuwa zai ce maka karya ne, karya ne, karya ne. Ina tuna a Kano ya gabatar da takarda a kan Daura, inda aka ce nan asalin Hausa yake, aka ce duk sarakunan Hausa duk wadanda ta haifa duk sarakuna ne. Ya ce ba a duba wannan  batu zai zama cewa duk wani Bahaushe dan sarki ne, duk wani Bahaushe dan sarauniya ne. Ya ce irin wannan batu mugun tunani ne. Ya ce idan an ce tatsuniya ce, to a bar ta a matsayin tatsuniyarta, domin kirkirarren abu ba na gaskiya ba ne. Na san sarkin Daura (Allah gafarta masa) yana zaune a wurin nan, amma Jinju ya ce yana bidar gafara daga gare shi, amma dai wannan ita ce gaskiyar. Hambali mutum ne wanda bai da tsoro kuma kokarin ya koya wa almajiransa komai yake iya koya masu. Ya yi ayyuka wurare da dama. A Najeriya, a Legas ya fara aiki, kafin ya dawo ya yi aiki a Jami’ar Bayero da Jami’ar Ahmadu Bello Zariya da kuma Jami’ar Usman danfodiyo Sakkwato. Aikinsa na Sakkwato shi ne na karshe, inda daga nan ya koma gida. Ya yi rubuce-rubuce, ya yi bincike mai dinbin yawa, ba ga harshen Hausa kadai ba, har da al’adun Hausa da magungunan Hausa da wadansu dabi’u na Bahaushe.
Daga karshe, wane kira za ka yi ga dalibansa domin su yi koyi da halayensa da kishinsa ga al’umma?
 In sun kasa yin irin hakurinsa, suka kasa yin karatu yadda ya rika ummurtar su, yana cewa a karanta, a karanta, a yi karatu, a yi bincike, suka kasa; to don Allah kada su bar aikin da ya bar musu ya lalace. Wannan ne kiran da zan yi.