Harshen Hausa na fuskantar barazana a Legas – Shugaban kungiyar AUGA
Shugaban kungiyar ’yan Arewa wacce ake kira Arewa United Gamji Association wato (AUGA), Aliyu Garba Tudu ya ce nan da ’yan shekaru masu zuwa yarukan mutanen Arewa na asali za su bata a Jihar Legas. Aliyu Garba Tudu wanda ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da Aminiya a jihar, ya ce yarukan Arewa na […]
Shugaban kungiyar ’yan Arewa wacce ake kira Arewa United Gamji Association wato (AUGA), Aliyu Garba Tudu ya ce nan da ’yan shekaru masu zuwa yarukan mutanen Arewa na asali za su bata a Jihar Legas.
Aliyu Garba Tudu wanda ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da Aminiya a jihar, ya ce yarukan Arewa na fuskantar kalubale a jihar saboda watsin da ’yan Arewa suka yi da yarukansu na asali.
“Mutanenmu na yankin Arewa da ke zaune a Jihar Legas sun yi watsi da yarukansu na asali da kuma al’adunsu na gargajiya. Za ka ga mutum dan Arewa da ka yi masa yarensa misali idan Bahaushe ne sai ya mayar maka da turanci, shi kuma ba jin turanci yake sosai ba. Wani ya mayar maka da Yarabanci. Wasu ma ba su son sanya tufafinmu na Arewa wai don kada a kira su Hausawa. To shi ya sa muke ganin cewa muddin ’yan Arewa suka tafi a haka ba su gyara ba to nan da shekara biyar yarukansu za su bace. Domin yaran da suka haifa za su taso ba sa jin yaren nasu,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “akwai abokina Basakkwace ne, amma ’ya’yansa takwas ba sa jin yarensa na Hausa mun kira shi mun ba shi shawara cewar ya rika yi musu harshen Hausa a gida, Turanci za su koya a makaranta, Yarabanci kuma za su koya a kan titi, amma ya ki ji. Muna ci gaba da ba shi shawara don ya gyara. Ka ga wannan ba karamin koma baya ba ne. Akwai kabilun Arewa da yawa da ’ya’yansu ba sa jin yarensu sai Yarabanci da turanci. To shi ya sa muka tashi tsaye muke fadakar da mutanenmu na Arewa su farga su gane kuskuren da suka yi.”
Ya ce saboda haka ne kungiyar ta dauki matakan shirya taruka da kuma yin bukuwan al’adun gargajiya domin fadakar da jama’a. Ya kara da cewa nasarorin da kungiyar ta samu sun hada da hada kan jama’a da sauran kungiyoyi da kuma gwamnati.
Da aka tambaye shi irin matsalolin da kungiyar ta ke fuskanta, sai ya ce matsalar tsaro da tsangwammar da ake yi wa ’yan Arewa a Jihar Legas. “Ana kiranmu da wasu sunaye kamar su Malam ko Mola da aboki da Boko Haram. Ba wani kabila da ake kira da haka sai mutanemu na Arewa. Saboda haka ne muka tashi tsaye don mu ga mun zare kanmu daga cikin wannan tsangwama da zargi da ake yi mana,” inji shi