Harshen Hausa ne na farko a Rediyo RFI – Bashir Ibrahim Idris

A makon jiya ne Sashen Hausa Na Rdiyon Faransa (RFI) ya cika shekara shida da fara watsa shirye-shiryensa ga al’ummar duniya. A yau, ke nan gidan rediyon ya cika shekara shida cur. To wai yaya aka yi tafiyar nan ta faro? Wakilinmu ya tattauna da Babban Editan Sashen Hausa na RFI, Malam Bashir Ibrahim Idris, […]

Harshen Hausa ne na farko a Rediyo RFI – Bashir Ibrahim Idris
Harshen Hausa ne na farko a Rediyo RFI – Bashir Ibrahim Idris

A makon jiya ne Sashen Hausa Na Rdiyon Faransa (RFI) ya cika shekara shida da fara watsa shirye-shiryensa ga al’ummar duniya. A yau, ke nan gidan rediyon ya cika shekara shida cur. To wai yaya aka yi tafiyar nan ta faro? Wakilinmu ya tattauna da Babban Editan Sashen Hausa na RFI, Malam Bashir Ibrahim Idris, wanda ya bayyana cewa, a duk yarukan Afrika, harshen Hausa ne na farko da gidan ya fara aiki da shi wajen watsa shirye-shiryensa, sannan kuma sai harshen Swahili ya biyo baya. Ga tattaunawar yadda ta kasance:

Malam Bashir, RFI Hausa ta cika shekara shida da fara watsa labarai a duniya, ta yaya tafiyar nan ta faro?
kasar Faransa ta fahimci muhimmancin harshen Hausa, yawan masu amfani da shi a duniya da kuma rawar da yake takawa wajen aikewa da sakonni, sai ta ga ta makara wajen kafa wannan sashe, yayin da Birtaniya da Amurka da Jamus da ma kasashe irinsu Sin da Iran da Sudan, duk sun mallaki sashen Hausa. Dalilin kafa tashar ke nan wadda ta fara watsa shirye-shirye a ranar 21 ga watan Mayu, 2007.
An fara wannan aiki a karkashin Lanni Smith, Shugabar Sashen, wadda kuma ta yi ruwa da tsaki wajen samun nasararsa. An bude tashar ne da ‘yan jarida biyar: Bashir Ibrahim Idris, a matsayin Edita, Mammane Barmou da Suleiman Babayo da Abdou Halilou da Adamou Maimota da Mahaman Salissou Hamissou. Kuma Hausa ce harshen Afrika na farko da Radiyo Faransa ta fara aiki da shi kafin Swahili daga bisani.
Wadanne nasarori kuka samu a tsawon shekarun nan?
Babbar nasara ita ce karbuwa daga jama’ar Hausawa da ma wadanda ba Hausawa ba da ke jin Hausar a ko’ina a duniya. Wannan na samuwa ta sakonni ta waya ko kuma wasikun da muke samu a kowace rana da kuma irin kalaman da masu sauraron ke yi dangane da tashar. Babu abin da za mu ce sai hamdala.
Wadanne kalubale da matsaloli kuka fuskanta a tsawon lokacin nan kuma ta yaya kuka ga bayansu?
Babbar matsala ko kalubalen da muka samu shi ne na janyo hankalin masu sauraro zuwa tashar tamu. Ga Bahaushe ko kuma mai jin Hausa, BBC, Muryar Amurka da DW Radio sun zama jiki saboda sabo da su, ganin shekarun da suka kwashe suna aiki amma da taimakon Ubangiji da dabarun sanya masu sauraro cikin shirin wajen bayyan ra’ayoyinsu da kuma bai wa jama’a damar bayani kan abin da ya faru a yankunansu, wadannan sun taimaka mana sosai.
Wadanne sabbin matakai ko shirye-shiryen za ku fito da su domin sake jan hankali masu sauraronku da nufin samun nasarorin da suka ninka na baya?
Masu sauraro sun dade suna ba da shawarwari kan wasu karin shirye-shiryen da suke bukata kuma muna shirin share masu hawaye nan ba da dadewa ba, kamar shirin amsoshin tambayoyinku da makamantan haka.
Ko kana da kira zuwa ga abokan aikinka da kuma masu sauraro dangane da ayyukanku?
Kirana ga abokan aiki shi ne, na farko tsage gaskiya komai dacinta. Domin a kodayaushe shugabanni da masu rike da kujerun mulki ba sa son ganin talaka ya san abin da suke yi ko kuma yadda suke taka masa hakki. Na biyu, a dinga bin ka’idar aiki, ba tare da son rai ba, koda kuwa labarin ya shafi muradunsu. Saboda haka fifita labarin da ya shafi al’umma ya zama wajibi. Su kuwa masu sauraro, duk da yake don su ake yi, yana da kyau su kuma su dinga hakuri da ma’aikata da kuma sake masu mara wajen gudanar da aikinsu.
Za mu so jin sunayen wasu zaratan shugabannin RFI Hausa da zaratan ma’aikatan da suka jajirce suka bayar da gudunmowa har kuka samu nasara a cikin shekara 6 kacal.
Daga kafa wannan sashe zuwa yanzu, an samu shugabannin gudanarwa uku, wato Lanni Smith da Emmanuel Dabzac da Julie bandal, mai ci yanzu. Ni kuma ni ne Editanta tun fara aikin zuwa yau, sai Garba Aliyu Zariya da ya fara aiki da mu a 2009, a matsayin mataimaki. Akwai irinsu Mamane Barmou da Suleiman Babayo da Adamou Maimota da Abdou Halilou da yau duk ba su tare da mu amma kuma sun bayar da gudunmmowa. Kana akwai Mahaman Salissou Hamissou da Awwal Janyau da Nasirudeen Muhammad da Hauwa Kabir da Faruk Muhammad Yabo da Abdoulaye Issa da Mahmud Lalo da Ramatu Garba Baba da kuma Abdulkarim Ibrahim. Akwai injiniyoyi irinsu Mustapha Adebisi da Ibrahim Tukur keffi da Umar Faruk Ibrahim.
Kana da wani karin bayani, wanda ban tambaye ka ba, dangane da tashar nan taku da ayyukanta?
Fatarmu a kodayaushe, ita ce gamsar da mai saurare. Kuma za mu yi iya bakin kokarinmu don ganin mun gamsar da mai sauraro a kodayaushe da ikon Allah. Kana a karshe muna yaba wa masu sauraronmu saboda hadin kan da suke ba mu a kodayaushe.

 

’Yan kwangila ne dalilin ɗauke wutar lantarki —EFCC

DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe