Harshen Hausa zai ci gaba da taka rawar bunkasa ilimi a Afrika da duk duniya – Khalid Imam

A kwanakin baya ne kungiyar ADEA tare da hadin gwiwar Global Book Alliance da kuma tallafin Hukumar USAID, suka shirya wani kwarya-kwaryan taron masu ruwa da tsaki a fagen samar da littattafai na ilimi a makarantun firamare da sakandare a Afirka, wanda aka gudanar a birnin Abidjan na kasar Kwaddebuwa. daya daga cikin mahalarta taron […]

Harshen Hausa zai ci gaba da taka rawar bunkasa ilimi a Afrika da duk duniya – Khalid Imam

A kwanakin baya ne kungiyar ADEA tare da hadin gwiwar Global Book Alliance da kuma tallafin Hukumar USAID, suka shirya wani kwarya-kwaryan taron masu ruwa da tsaki a fagen samar da littattafai na ilimi a makarantun firamare da sakandare a Afirka, wanda aka gudanar a birnin Abidjan na kasar Kwaddebuwa. daya daga cikin mahalarta taron daga Najeriya, shi ne Khalid Imam, malamin makaranta kuma fitaccen marubuci. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana yadda taron ya gudana:

Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja

 

Ka halarci taron da ka wakilci Najeriya da kuma harshen Hausa, ko za ka iya yi mana bayani game da taron a takaice?

Babu shakka kamar yadda ka ambata, na wakilci Najeriya da kuma harshenmu na Hausa wanda, alhamdu lillahi, shi kadai ne harshen da masu shirya taron suka ga cancantar zabensa domin ya wakilci sauran harsunan da ake magana da su a kasarmu ta Najeriya a wajen wancan muhimmin taro da aka gudanar na kasashen Afirka a birnin Abidjan da ke can kasar Kwaddebuwa a ranakun 22 zuwa 25 ga watan Janairu na shekarar 2018.

A taron, an gayyaci kasashe guda goma-goma na Afirka masu magana da harsunan Ingilishi da Faransanci. Kuma taro ne da kungiyar samar da ci gaba a fagen ilimi a kasashen Afirka (Association for the Debelopment of Education in Africa – ADEA) tare da hadin gwiwar Global Book Alliance da kuma tallafin Hukumar USAID suka shirya.

A taron na kwanaki hudu, masana daga ko’ina a duniya sun gabatar da mukalu kan yadda za a samar da sababbin littattafan ilimi da na koyarwa, wadanda suka dace da zamani da addini da kuma al’adun mutanen Afirka domin bunkasa harkar koyo da koyarwa a kasashen Afirka. Taron ya samu halartar wakilan Bankin Duniya da mashahuran masana daga jami’o’i daban-daban na duniya da wakilan hukumomin ilimi na kasashen Afirka  da masu harkar wallafa littattafai da dillalansu a kasashen Afirka da kuma marubuta, musamman masu yin rubutu cikin wasu manyan harsunan Afirka kamar Hausa da Swahili da Bantu da sauransu.        

Me ya gudana a taron?

A gaskiya kamar yadda na fara bayani, wannan taro da na halarta taro ne da ya tattara masu ruwa da tsaki domin tattauna matsaloli da samar da mafita don inganta harkar samar da littattafai domin makarantu. Haka kuma, an yi bitar matsalolin da suka dabaibaye harkar samar da littattafai wadanda suka hada da rashin isassun kwararrun marubuta da kuma haraji da gwamnatocin kasashen Afirka suke dora wa masu ruwa da tsaki a fagen wallafa da sayar da littattafai na koyo da koyarwa a makarantun firamare da na gaba da firamare a Afirka.

Bugu da kari, an koyar da mahalarta taron sabbin dabaru da hanyoyi na zamani da za su saukaka samar da ingantattun littattafai domin inganta harkar koyo da koyarwa a kasashen Afirka, musamman duba da cewa sauran sassan duniya tuni sun yi gaba a wadannan fagage ta yin amfani kimiyyar da zamani ya samar (Digital Publishing). Har ila yau, an koyar da mahalarta taron sabbin hanyoyin samar da matanoni na ilimi a cikin harsunan Afirka da kuma yadda ’yan Afirka masu kamfanonin wallafa za su samar da hadin gwiwa a tsakaninsu wato da kuma samarwa tare da yada littattafan da za a dinga fassarawa a harsunan Afirka, musamman wadanda ake koyar da su a makarantu.

Wanne tasiri harshen Hausa ya yi a wajen taron?

Kamar yadda kowa ya sani, harshen Hausa harshe ne na duniya kuma a wajen taron ya taka muhimmiyar rawa, musamman a lokacin da mahalarta taron suka rarrabu zuwa kananan kwamitoci domin tattaunawa da fito da shawarwarin da za su zama matsayar mahalarta taron. Ni da na wakilci Najeriya da kuma Malam Bako daga makwabciyar kasarmu ta Nijar, mun zama masu yin tafinta cikin Hausa ga sauran ’yan uwanmu ’yan kwamiti na musamman da aka kafa don inganta koyo da koyarwa da harsunan Afirka, kasancewar ’yan kwamitin sun fito ne daga kasashen da ke amfani da harshen Ingilishi da Faransanci. Ban da rawar da harshen Hausa ya taka da tattaunawa a wannan zama, ta yi matukar wahala musamman saboda an gudanar da shi ne a dakin taron da babu na’urar da take fassara batutuwan da aka tattauna. Saboda tasirin da harshen Hausa ya yi a wannan zauren, Farfesa Pascal Kishindo na kasar Malawi ya bayyana farin cikin tasirin da harshen Hausa ya yi karara, duk da cewa shi kwararre ne a fagen amfani da harshen kasarsa, wato Bantu   

Wanne tagomashi kake ganin harshen Hausa zai samu a duniya sanadiyyar wannan taron?

Ko shakka babu, harshen Hausa zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa a Afirka da kuma duniya, musamman duba da cewa mahalarta taron sun gamsu cewa ilimi a Afirka ba zai samu ba da kuma samar da ci gaban da ake bukata har sai an koma amfani da harsunanmu na gida, wanda tuni harshen Hausa ya yi fice a wannan fage na zama zakaran-gwajin-dafi. Kuma kamar yadda kowa ya sani, rubutu cikin harshen Hausa don amfanin makarantu a kowane mataki na ilimi ba abu ne sabo ba, sai dai kawai akwai bukatar masu ruwa da tsaki a fagen su sake zage dantse duba da cewa Hausar dai ita ce har yanzu jagora a wannan fage, ba wai kawai a Najeriya ba, har da sauran kasashen Afirka.

Ko akwai wani shiri da ya gudana dangane da rubuta da marubutan Hausa a wajen taron?

Kamar yadda na bayyana a baya, taron kacokan an shirya shi ne don inganta harkar rubutu da kuma tallafa wa marubuta, musamman masu amfani da harsunan Afirka wanda Hausa ita ce a kan gaba. Sannan taro ne wanda a nan gaba zai taimaka sosai wajen bunkasa rubutu da Hausa. Abin albishir ga masu karatu shi ne, sakamakon bayanan da muka yi a wajen taron kan yadda Hausa ke ba da gudummawa wajen inganta ilimi, Allah cikin ikonSa, an amince za a gudanar da taro a Najeriya makamancin wanda na halarta a nan kusa, musamman ga marubuta Hausa masu rubutu domin samar da littattafan yada ilimi a makarantun firamare da sakandare.

Wacce rawa kake ganin ya kamata masana harshen Hausa su taka don kara bunkasa harshen a duniya, bisa la’akari da wannan taron da ka halarta?

Kiran da zan yi a nan shi ne, mu Hausawa ya zama wajibi mu farka mu fahimci irin albarkar da Allah Ya yi wa harshenmu na Hausa, da kuma irin darajar da sauran wadanda ba Hausawa ba suke daukarsa da shi. Domin dai duk wanda ya sha dadin inuwar gemu bai kai makogwaro ba, wato duk wanda zai amfana da Hausa ba fa ya mu ba masu harshen. Tabbas, lokaci ya yi da za mu daina watsi da darajar da Allah Ya yi wa harshenmu, mu kuma daina raina shi muna ganin wanda duk ba Turanci ya iya ba ko yake yi, ba mai ilimi ba ne. Hakika, damar da na samu ta halartar wannan taro ta kara tabbatar mani cewa duk inda giwa ta kada itace, to tabbas shi ma zomo zai kada ciyawa. Abin nufi a nan shi ne, duk inda Ingilishi ko wani harshe zai taka rawa, to harshen Hausa ma ba za a bar shi a baya ba. 

Ko wacce shawara za ka bayar musamman ga shugabanni da attajirai da talakawan Arewa dangane da harshen Hausa?

Shawarata a nan ba ta wuce cewa shi fa hannu daya ba shi daukar jinka. Wato wajibi ne, muddin muna son mu sauke nauyin da ya rataya a kanmu na bai wa Hausa gudummawar da ta dace domin habakarta da sake yaduwarta a duniya, to lokaci ya yi da shugabanni da attajirai da marubuta cikin harshen Hausa da kuma talakawan Arewa da na sauran kasashen da ke amfani da harshen Hausa kamar su Nijar da Kamaru da Ghana dukkanmu mu fahimci cewa shi fa kayan aro abin banza ne. Ashe ke nan ba daidai ba ne mu ci gaba da dogaro da cewa sai Turawa ne za su rika yi wa harshen Hausa gata. Mu me muke yi? Ya kamata kuma mu fahimci cewa shi fa harshe tamkar gona ce sai da kulawa, muddin ana son gonar nan ta yi yabanya. Ashe ke nan muddin muna son harshenmu ya zama jagora, sai mun tashi mun habaka shi. 

Ko kana da wani karin bayani game da taron, wanda ban tambaye ka ba?  

E to, abin da zan kara shi ne, shi dai wannan taro, taro ne na kokarin samar da mafita ga Afirka, kuma an fada wa juna gaskiya cewa duk al’ummar da ta ci gaba ta samu nasarar hakan ne ta yin amfani da harsunanta. Ke nan babban sako da na zo mana da shi daga wajen wannan taro shi ne, makomar Afirka a fagen ilimin kimiyya da fasaha da sauran fannonin ilimi tana ga hannun ’yan Afirka. Kuma ’yan Afirkan da suka taru da sauran masana daga sassan duniya duk sun gamsu cewa ci gaban Afirka na da alaka ta kut-da-kut ga rungumar harsunanmu na Afirka kamar Hausa; musamman a fagen amfani da su wajen yada ilimi da koyo da koyarwa a makarantunmu. Kuma taron ya yi kira ga gwamnatoci na Afirka su fahimci haka, su kuma karfafi wannan kokari da aka fara na dasa dan-ba a birnin Abidjan.

 

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa