Harshen Uwa
Kullum nakan yi tunani mai zurfi, in yi ajiyar zuciya, sannan in kuta. Nakan tuna da a ce tun lokacin da na shiga firamare da harshen Hausa aka rika koya mini ilimi da yaya zan kasance? Ba ni kadai ba, shin kai ko ke ma, da a ce da harshenku ake koya muku ilimi tun […]
Kullum nakan yi tunani mai zurfi, in yi ajiyar zuciya, sannan in kuta. Nakan tuna da a ce tun lokacin da na shiga firamare da harshen Hausa aka rika koya mini ilimi da yaya zan kasance? Ba ni kadai ba, shin kai ko ke ma, da a ce da harshenku ake koya muku ilimi tun daga firamare zuwa sakandare zuwa jami’a, shin yaya al’amarinku zai kasance?
Misali idan an zo batun Kimiyya, a ce wane, dauki sinadarin can kore, ka hada shi da ruwa daidai kaza ka girgiza shi, zai ba ka sinadari kaza Shin ko kwakwalwar jakai gare ka ba za ka fahimta ba?
Misali na biyu, a ce an zo kan Lissafi, darasin da ke jigata dalibai da yawa, malamin ya zayyano bayaninsa da tsagwaron Hausa, shin zan fahimta ko ba zan fahimta ba?
Amma ina! An hana mu, an yi mana fashin fasaha da karfi da yaji, an kakaba mana bauta. An sanya mu kan dole sai mun yi magana da bakon harshe, sai mun yi sauraro da bakon harshe, sai mun yi tunani da bakon harshe. Hatta fahimtar al’amura ma, an sanya mu dole sai da harshen wadansu za mu yi hasashe.
Abin da haka ke nufi shi ne, idan tunani ya zo maka, sai ka fassara shi da Ingilishi, sannan ka sarrafa shi a aikace zuwa abin da kake so. Amma da ba haka ba ne, da harshenka za ka yi tunani, ka antayo shi kai-tsaye. Shin wannan ba shi ake kira orijina ba?
Ya kamata mu tattaru mu yi karatun-ta-natsu. Ya kamata manyanmu, masananmu su tattaru su kwato mana hakkinmu, mu dawo gida, mu rungumi harshenmu na gadon gado. Masu iya magana suna cewa, kayan aro abin banza ne, ranar da mai abin ya nemi abinsa, dole za ka dawo naka. Kowa ya bar gida, gida ya bar shi.
Ya kamata mu fahimta cewa babu yadda kasa da al’ummarta za su ci gaba da harshen aro. Ya zama wajibi Najeriya mu yi koyi da kasashen da suka ci gaba a fannin kimiyya da kere-kere a zamanin nan. Ina maganar kasashe kamar Japan da China da Indiya da Indonesiya da irinsu. Sai da suka rufe ido suka rika amfani da harsunansu a harkar ilimi da ilimantarwa sannan suka samu sa’ida. ko mun shirya amsar gaskiya kuwa?