Harsuna 5 da aka fi amfani da su a Yammacin Afrika

Akwai harsuna akalla 2,000 a Yammacin Afrika, amma wadannan suka fi yin fice.

Harsuna 5 da aka fi amfani da su a Yammacin Afrika

Akwai harsuna sama da 2,000 a nahiyar Afirka, inda a Najeriya kadai akwai sama da yare 200.

Amma a Yammacin Afirka, akwai wasu harsuna da suka yi fice kuma aka fi amfani da su wajen harkokin yau da kullum.

Aminiya ta yi nazari kan irin waddannan harsunan kuma ta zakulo muku guda biyar da aka fi amfani da su a yankin.

1. Faransanci

Harshen Faransanci na daya daga cikin fitattun harsuna da ake amfani da su a Yammacin Afrika, musamman a kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.

Akwai sama da mutum miliyan 50 da ke magana da harshen, kuma kasashe 11 daga cikin kasashe 16 na yankin na amfani da shi.

Kasashen da suke amfani da Faransanci sun hada da Jamhuriyar Nijar, Togo, Senegal, Mali, Burkina Faso, Kwaddibuwa, da dai sauransu.

2. Ingilishi

Harshen Ingilishi shi ne harshe na biyu a jerin harsunan da aka fi amfani da su a mafi yawan kasashen Yammacin Afrika.

Kasashen da ake amfani da Ingilishin sun hada da Saliyo, Ghana, Najeriya, Laberiya da Gambiya.

3. Hausa

Harshen Hausa ya yi fice kuma yana da mutane sama da miliyan 27 da ake amfani da shi musamman a wasu kasashen Yammacin Afirka da suka hada da Arewacin Najeriya, Kudancin Jamhuriyar Nijar, Ghana, Togo da sauran wasu kasashen a nahiyar Afrika.

4. Larabci

Larabci na daya daga cikin harsunan da wasu kasashe ke amfani da shi. A kasar Mali da Mauritaniya, suna amfani da shi a matsayin harshe na musamman kuma harshen kasa. Kazalika, yana daga cikin harsunan da suka yadu cikin kankanin lokaci a Afirka.

5. Yarabanci

Ana hasashen cewa Yarbanci na da mutum sama da miliyan 20 da ake amfani da shi a nahiyar Afirka kuma daga cikin manyan harsuna uku da ake amfani da su a Najeriya.

Kasashe irin su Jamhuriyar Benin, Togo, Laberiya, Saliyo da wasu kasashe na amfani da Yarabanci.