Hasashe: Abubuwan da ka iya faruwa bayan zaben 2015

Mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka, inji ’yan magana. Yana da kyau mu kalli zaben 2015 da ke tafe, mu kuma fada wa kanmu gaskiya.Ga duk wanda ya kalli yadda siyasar 2015 ke tafiya, ya san cewa babu wani abu da zai iya hana wa Jonathan cin zaben sai kADDARA, domin alamu sun […]

Hasashe: Abubuwan da ka iya faruwa bayan zaben 2015
Hasashe: Abubuwan da ka iya faruwa bayan zaben 2015

Mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka, inji ’yan magana. Yana da kyau mu kalli zaben 2015 da ke tafe, mu kuma fada wa kanmu gaskiya.
Ga duk wanda ya kalli yadda siyasar 2015 ke tafiya, ya san cewa babu wani abu da zai iya hana wa Jonathan cin zaben sai kADDARA, domin alamu sun tabbatar da cewa muddin an zuba zabe sai ya koma shugabanci a karo na biyu, ko da kuri’ar halal ko ta haram.
Yanzu alamu sun nuna cewa Shugaban kasa ya fi ’yan hamayya kwarin gwiwar cin zabe mai zuwa, domin take-takensa sun nuna haka. A yayin da a gefe guda, masu ikirarin hamayya basa nuna wani kwarin gwiwa a kan zaben, idan ban da hayaniya a jaridu da intanet. To mai zai faru idan Shugaban kasa ya kuma cin zabe? Wannan wata muhimmiyar tambaya ce da mutane da dama za su iya bayar da amsarta, idan aka dubi abin da ya biyo bayan sakamakon zaben 2011.
Abu biyu ne za su iya faruwa idan ya wuce a karo na biyu. Na farko shi ne irin misalin abin da ya faru a kasar Thailand, inda masu adawa da Shugaban kasar Yunlak Shinwatra suka fito kan tituna suna bore. Sai da ta kai masu boren sun dangana har zuwa fadar Shugaban kasar, inda suka yanke wutar lantarkin da ta shiga fadar, suka sanya siminti suka tottoshe kofofin shiga fadar, suka farfasa tagogi da gilasai da daddaye tayil din da aka shimfida a kan tituna, suka yi zaman dirshan, ba shiga ba fita har dai daga karshe suka saduda suka koma gidajensu, ba tare da bukatarsu ta tunbuke shugabar ta biya ba.
Na biyu shi ne abin da ya faru a kasar Ukraine, inda masu bore suka fito cikin tsananin sanyin dusar kankara suna kiran Shugaba bictor Yunokobich ya sauka; wanda daman sun taba yin haka a 2004, inda suka kori Shugaban lokacin, Yushechenko. Sun kona tayoyi tare da banka wa gine-ginen gwamnati wuta, har dai shugaban ya arzce, ya kama gabansa. Masu bore suka ci nasarar fatattakar Shugaban kasa, wanda hakan ya yi sanadiyyar ballewar yankin Crimea, inda kasar Russia ta mamaye yankin, duk da cewa ba shi da wani muhimmanci ta fuskar tattalin arziki, ba zai nakasa Ukraine ba ko da kuwa ya koma karkashin Rasha.
daya daga cikin biyun nan na iya faruwa a Najeriya bayan zaben 2015. Ko dai masu bore su ci nasarar korar Shugaban kasa kamar yadda ya faru a Ukraine, wanda abu ne mai kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, ko kuma irin abin da ya faru a kasar Thailand ya faru a Najeriya, masu zanga-zanga bayan sun gama bore a titunan biranen Kano da Kaduna da Bauchi da Sakkwato da Katsina su koma gida bayan sun gama artabu da jami’an tsaro, wadanda za su mutu sun mutu, wadanda za su karye sun karye, a zuba wa Sarautar Allah ido, a kuma yi tunanin tarawa a 2019 ga mai yawan rai.
Babban abin tsoron, shi ne barkewar rikicin kabilanci da na addini a musamman jihohin Arewacin Najeriya, wanda za a shiga gaba kura ne…, don ga hare-haren da ake cewa ba a san ko su waye suke kai wa ba kuma ga al’amuran bayan zabe. Allah Ya kiyaye, Ya kare asarar dukiya da ta rayuka.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno