Hasashen manyan abubuwan da za su faru a Kannywood a 2022
Aminiya ta yi hasashen wasu abubuwa da za su dauki hankali a Masana’antar a bana.
Masana’antar Kannywood masana’anta ce da take jan hankalin mutane, musamman ma matasan Arewa kamar yadda takwararta ta Nollywood take a yankin Kudu.
A shekarun baya, musamman shekara hudu zuwa biyar da suka wuce, masana’antar ta shiga mawuyacin hali, har wadansu daga cikin masu ruwa- da-tsaki a cikinta suka fara tunanin za ta durkushe, ganin kasuwancin masana’antar ya tabarbare matuka.
- Bayan wata 11 cikin duhu, an dawo da wutar lantarki a Maiduguri
- An sako daliban FGC Yauri 30 da malaminsu bayan kwana 207 a hannun masu garkuwa da su
Wadansu sun koma wata sana’ar, wadansu kuma sun hada da wata. Da dama daga cikin masu shirya fim suna da fina-finai da tsoron asara ya sa suka ajiye fina-finan ba su fitar ba.
Sai dai yanayin sauyi da ci-gaban zamani, musamman ta Intanet ya sa wadansu sun dawo da karfinsu, inda a yanzu haka harkoki suke ta dawowa a hankali.
Don haka ne Aminiya ta yi hasashen wasu abubuwa da za su dauki hankali a Masana’antar Kannywood a bana:
Komawa YouTube
Kamar yadda aka sani, yanzu haka fina-finai da dama masu jan hankali a yau yawancinsu a kafar YouTube ake nunawa.
A da can kananan fina-finai ake haskawa a kafar, amma yanzu manyan masu shirya fina-finai sun fara komawa kafar domin cin moriyarta tare da tafiya da zamani.
Yanzu haka ana haska fim din
Kamfanin FKD na Ali Nuhu mai suna Alaka a YouTube, sannan akwai fim din Bintu wanda za a fara haskawa a bana na kamfanin Abubakar Bashir Maishadda.
Lura da yadda haska fina-finai a
sinima ke tafiyar hawainiya da yadda ake raba riba da masu sinimomin da kuma karancinsu, sannan da kuma cewa kyauta ake dora fina-finai a YouTube, kuma ana kallo ne su biya ka, don haka Aminiya na hasashen cewa masu shirya fina-finai da dama za su koma YouTube da haska fina-finansu.
Darakta mace
Tun a shekarar 2020 ce ya kamata jaruma Nafisat Abdullahi ta bayar da
umarnin fim dinta mai suna Zainab Ali a kamfaninta mai suna Nafs Entertainment, amma hakan bai yiwu ba saboda yanayin yadda duniyar ta shiga rudu.
Jarumar ce ta dauki nauyin fim din Yaki A Soyayya da ya yi tashe sosai a shekarar 2019, wanda tun bayansa ne ta fara shirye-shiryen zama darakta a masana’antar.
Wadansu na ganin bayar da umarni
aiki na maza ne, domin yana bukatar
juriya da karfin hali.
Sai dai Aminiya ta gano cewa tsohuwar jaruma Muhibbat Abdulsalam, wadda matar darakta Hassan Giggs ce ta zama mai bayar da umarni a Kannywood.
Nafisat ta yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje domin karo karatu da shirye-shirye.
A cikin dalilinta na ficewa daga shirin
Labarina mai dogon zango na Aminu
Saira, ta bayyana rashin isasshen lokaci da karatu da kuma fim dinta da take aiki a kai a matsayin wasu daga dalilanta na ficewa daga fim din.
Kasancewar yanzu masana’antar ta fara farfadowa, sannan batun cutar Kwarona ta fara kwantawa da yanayin karatuttukan da jarumar ta yi da kuma tafiye-tafiyen da ta yi, akwai yiwuwar
ta shirya tsaf domin zama cikakkiyar
darakta a masana’antar ta Kannywood.
Dawowar jaruma Maryam Yahaya
Maryam Yahaya fitacciyar jaruma
ce a masana’antar da a bara ta sha fama da matsananciyar jinya. Sai dai a yanzu jarumar ta warke garau, kuma alamu sun nuna a shirya take ta dawo taka rawa a masana’antar.
Sababbin jaruman da za su ja masana’antar
A wani sabon lamari kuma, kasancewar an dade ana ganin fuskokin da yawa daga cikin jaruman masana’antar, sai wadansu masu kallo suke ganin lokaci ya yi da za a fara ganin sababbin fuskoki.
An dade ana korafin cewa wadanda aka fi ganin su din ne ba sa so wadansu su shigo, su kuma suna cewa kowa na da gurbinsa, inda a bangaren masu shirya fina-finai suke tunanin ribar da za su samu idan suka shirya fim babu manyan jarumai.
Sai dai komawa YouTube ya ba da
damar yin amfani da kanana da sababbin jarumai, inda fina-finai da dama sababbin jarumai ne ke jan su.
Wannan ya sa Aminiya ta rairayo wadansu jarumai da take ganin za a fi jin su a bana.
Mommee Gombe
A bara ce jaruma Mommee Gombe ta fara jan zarenta a Kannywood bayan
fitowarta a bidiyon wakar Jarumar Mata tare da mawaki Hamisu Breaker.
Kafin nan, tana fitowa a wakoki, amma ba a santa sosai ba, a barar ta fara jan fina-finai manya a masana’antar.
Daga cikin fina-finan da ta fito akwai
Zainabu Abu da Sarki Goma Zamani Goma.
Yanzu haka, akwai ta cikin fim din Alaqa mai dogon zango na Ali Nuhu da sauran fina-finai masu dogon zango da ake shiryawa, kuma ita ma tana shirya nata fim din mai dogon zango.
Daddy Hikima
Asalin sunansa Adam Abdullahi Adam, amma yanzu an fi saninsa da Abale ko Ojo, saboda rawar da ya taka a fim din A Duniya na Tijjani Asase ko kuma shirin Haram.
A baya an fi saninsa da Daddy Hikima kuma ya yi fice a Masana’antar Kannywood ce a matsayin mai tsara
dandalin shiri ko aikin ci gaban shiri.
Sai dai tun bayan fim din A Duniya da ya fito a matsayin dan daba da Haram, sai ya zama fina-finai da dama suna nema masa gurbi.
Daga cikin fina-finan da suka yi masa gurbi akwai Labarina da Farin Wata da sauransu.
Yanzu haka akwai fim din Sanda wanda shi ya ja zaren da kuma wasu fina-finan da dama da Abalen ne zai ja a bana.
Fa’iza Abdullahi
Fa’iza Abdullahi sabuwar jaruma ce da sunanta ya fara shiga bakin masu kallon fina-finan masana’antar.
Ta fito a fina-finai da dama, ciki har da Gargada, inda take cikin manyan jaruman fim din, sannan tana cikin fim din Alaka na Ali Nuhu.
Tana cikin sababbin jaruman da masu shirya fina-finai da dama za su yi rububi a bana.
Rukky Alim
Sunanta na asali Rukayya Ahmed Aliyu, amma an fi saninta da suna Rukky Alim a Masana’antar Kannywood.
Matashiyar jaruma ce da a yanzu hakata fara jan zarenta a masana’antar.
Tana cikin fim din Asin da Asin na
Adam A. Zango da za a fara haskawa a bana da Ruwa Biyu da sauransu.
A’isha Najamu
A’isha Najamu ko A’isha Izzar So kamar yadda aka fi saninta, ta fara tashe ne a fim din Izzar So mai dogon zango.
Bayan nan ta fito a fina-finai da dama
irin su Sarki Goma Zamani Goma.
Tana cikin jaruman da ake tunanin za su ja fina-finai a bana.
Akwai irin su mawakiya Mufeedah
da a yanzu haka ita ce sabuwar Salma a fim din Kwana 90 da Rayya Aminu da sauransu.