Hasashen WHO kan dawwamar coronavirus na iya tabbata –Masana

Hasashen da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi cewa akwai yiwuwar coronavirus ta dawwama ka iya zama gaskiya in har kasashe ba su yi abin da ya dace ba, inji masana kiwon lafiya. Mai rikon mukamin Babban Darakta a Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Shiyyar Yammacin Afirka (RCDC), Farfesa Abdulsalam Nasidi, shi […]

Hasashen WHO kan dawwamar coronavirus na iya tabbata –Masana

Farfesa Abdulsalam Nasidi shugaban Hukumar yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Yammacin Afirka

Hasashen da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi cewa akwai yiwuwar coronavirus ta dawwama ka iya zama gaskiya in har kasashe ba su yi abin da ya dace ba, inji masana kiwon lafiya.

Mai rikon mukamin Babban Darakta a Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Shiyyar Yammacin Afirka (RCDC), Farfesa Abdulsalam Nasidi, shi ne ya fadi hakan a wata tattaunawa ta musamman da Aminiya ranar Alhamis.

Gargadin na WHO na zuwa ne a daidai lokacin da kasashe da dama suke kokarin sassauta dokar zaman gida da suka kakaba don takaita yaduwar cutar.

Hukumar ta yi gargadin cewa matakin ka iya kawo koma-baya a yakin da duniya ke yi da cutar, tana mai cewa cutar na iya zama har illa-masha-Allahu.

Dole a bi shawarar masana

Farfesa Nasidi ya ce ya zama wajibi kasashe su ci gaba da bin shawarwarin masana kiwon lafiya in har suna so su fatattaki cutar daga doron kasa.

Nasidi, wanda kwararre ne a bangaren cututtuka masu yaduwa, ya kara da cewa bisa la’akari da barazanar cutar a duniya, sassauta dokokin zaman gida a wannan lokacin na iya mayar da hannun agogo baya.

“Mun sani hakika mutane, musamman a kasashe masu tasowa irin Najeriya, na fama da matsin tattalin arziki sakamakon wannan dokar, amma duk da haka ya kamata mutane su fahimci cewa rayuwarsu tana da muhimmanci sama da komai.

“Idan alal misali cutar za ta kashe mutane 1,000, idan aka hakura aka zauna a gida, barazanar mutuwar na iya raguwa zuwa mutane dari kacal”, in ji Farfesa Nasidi.

Masanin ya kuma shawarci al’umma da su ci gaba da bin shawarwarin masana kiwon lafiya ta hanyar wanke hannuwansu a-kai-a-kai, gujewa shiga cunkoso da kuma zama a gida, yana mai cewa in dai ba hakan aka yi ba, to akwai yiwuwar hasashen na WHO ya tabbata.

Game da maganin coronavirus

Da ya juya kan maganin cutar da wasu suka yi ikirarin samarwa ciki har da kasar Madagascar, Farfesa Nasidi ya ce dole sai an yi taka-tsan-tsan wajen tabbatar da sahihancin maganin ta hanyar bincike kafin a amince da shi don guje wa jefa rayukan al’umma cikin hadari.

“Mu a kimiyyance idan ka yi ikirarin samo wani magani sai mu umarce ka da ka kawo mu tabbatar da ingancinsa a dakin gwaje-gwaje.

“Idan muka ga ba shi da wata illa sai mu amince da shi, amma idan muka ga wani abin da zai cutar da mutane to tabbas ba za mu sahale wa mutane su yi amfani da shi ba”, a cewarsa.

Cutar ta coronavirus dai ta fara bulla ne a birnin Wuhan na kasar China, kuma zuwa yanzu ta kama mutane sama da miliyan hudu da dubu dari biyu yayin da ta hallaka kusan mutum 300,000 a fadin duniya.