Haskaka wa ’yan mata hanyar shiga a dama da su a fannin shari’a (2)

Me ya sa za a karanta shari’a maimakon sauran darussa? Darasin shari’a ko dokoki na daga cikin darussan da suka shafi dukkan darussa. Idan kika karanta shari’a za ka iya samun haske kan sauran darussa. Shari’a ta shafi komai. Nazarin shari’a yana fadada tunanin da za ki iya nazarin magunguna da sauran darussan kimiyya da […]

Haskaka wa ’yan mata hanyar shiga a dama da su a fannin shari’a (2)
Haskaka wa ’yan mata hanyar shiga a dama da su a fannin shari’a (2)

Me ya sa za a karanta shari’a maimakon sauran darussa?

Darasin shari’a ko dokoki na daga cikin darussan da suka shafi dukkan darussa. Idan kika karanta shari’a za ka iya samun haske kan sauran darussa. Shari’a ta shafi komai. Nazarin shari’a yana fadada tunanin da za ki iya nazarin magunguna da sauran darussan kimiyya da suke da alaka da dokoki, ko dokar hakkin mallaka a bangaren adabi ko yarjejeniyar tattalin arziki da dokar kwantaragi ko dokokin siyasar yankuna a karkashin dokokin kasashen duniya ko halayen dan Adam a cikin dokokin iyali da sauransu.
Shari’a ko dokoki za su jagorance ki ga bunkasa kwarewarki a fannoni da dama. Tana kalubalantarki ki fadada tunaninki, ki karfafa fahimtarki tare da zurfafa iliminki a sauran kwasa-kwasai na sanin dan Adam da kimiyyar rayuwa. Idan kika karanci shari’a za ki bunkasa himmarki ta zurfafa tunani da dabarun warware matsaloli a aikace. Wannan kwarewa ana samunta ne ta hanyoyi da dabaru daban-daban na fasaha da koyarwa da koyo: Misali hanyar Sokaret (Socratic Method) na muhawara da daddalewa da koyarwa da fasalin muhawarar kotu, inda ake bunkasa fahimta ta hanyar gabatar da magana ta ingantaccen tunani da muhawarar baka da sauransu.
Darasin likitancin shari’a kan bayar da karin horo ga dalibai su dada samun kwarewa da bayar da shawara da tallafi ga mutanen da suke da matsala ta gaskiya.
Idan kika samu horo a bangaren shari’a, kin fi samun dama ta kaiwa kololuwa a bangaren da kika zaba don yin aiki. Koda a Arewa da ake yi mata kallon baya ga dangi, matan da suka fito daga Arewa sun rike manyan mukamai a bangaren shari’a. wannan ba zai rasa nasaba da cewa babu batun cewa wannan mace ce a bangaren shari’a. Idan kika tsallake wahalar samun horo har kika zama lauya, babu batun ‘ke mace ce.’ Wasu daga cikin matan Arewa da suka yi fice a matsayin lauyoyi sun hada har da Babbar Jojin Najeriya da ta gabata, Mai shari’a Maryam Aloma Mukhtar (shekarar 2012-2014), wadda ’yar Jihar Kano da kuma Shugabar Kotun daukaka kara ta Tarayya mai ci, Mai shari’a Zainab Bulkachuwa wadda ta fito daga Jihar Gombe da tsohuwar Babbar Jojin Jihar Kaduna Mai shari’a Rahila Hadea Cudjoe da Babbar Jojin Jihar Sakkwato a yanzu Mai shari’a A’isha Sani dahiru.
Sauran sun hada da Babbar Jojin Jihar Neja Mai shari’a Fati Abubakar da Mukaddashiyar Babban Jojin Jihar Kano, Mai shari’a Patricia Mahmoud.
A bangaren koyarwa, matan Arewa sun samu wakilci sosai, misali fitacciyar Farfesar nan, Farfesa Hauwa Ibrahim ta Jami’ar Harbard da Jami’ar Cambridge da Jami’ar Massachusetts a Amurka ta fto ne daga Jihar Gombe.
Baya ga samun aiki a bangaren shari’a, kina iya samun dama a nada ki a mukamin da yake bukatar cikakken tunani a bangaren tabbatar da doka ko koyarwa ko kungiyoyin kasashen duniya ko kasuwanci a tsakanin kasashen duniya. Sannan akwai dimbin ayyuka da doka ta kebance su kawai ga wadanda suka karanta bangaren shari’a, misali mukamin Babban Rajistar Hukumar yi wa Kamfanoni Rajista ta kasa (CAC) da sauran kwararru da mukaman sakatarorin kamfanoni. Baya ga haka kowane lauya ya cancanci zama babban lauyan jiha ko na tarayya, kuma koda ba burinki ne ki karanta shari’a don zama lauya ko alkali ba, kina iya samun abin rayuwa daga aikin bayar da shawarwari. Kuma a cikin al’umma mai karancin tsare-tsaren inganta jin dadin jama’a da hanyoyin kare rayuka, wannan bangare na aikin zai iya samar miki da kudin shiga a bayan kin yi ritaya daga aiki.
Kuma kina da dama mai kyau ta hanyar horon da kika samu ki zama mai shiga tsakani don sasantawa. Wannan galibi yana faruwa da mata. A matsayinki na ’ya ko ’yar uwa ko matar aure ko uwa, kullum a sulhunta rigingimu kike. Kuma baya ga basirar da Allah Ya hore miki, ilimin da kika samu da horo a fannin shari’a da kika samu za su shirya ki ga fuskantar wannan kalubale.
Daga abin da ya gabata, za ki iya ganin cewa akwai dimbin alheri a cikin karantar aikin lauya ko shari’a. Kuma a matsayin ’yan mata ko matan aure, mun tagaza, amma har yanzu akwai karin kalubale da suke yi mana tarnaki wajen ci gaban diya mace. Tabbatacciyar hanyar da za ki kawar da wannan matsala ita ce ki samu kwarewa ko ilimin da zai ba ki dama a iya saurarenki a kowace kotu a Najeriya, ki yi magana kan duk abin da ya faru tare da tabbatar adalci a tsakanin al’umma. Ki tuna koda alamar shari’a an gabatar da ita ce a siffar “Mai Shari’a mace.” Don haka ki karanta shari’a ko zama cikakkiyar lauya za ki yi farin ciki da haka.

Dokta Balkisu Sa’idu
Sashin Shari’a na Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato. Ta gabatar da wannan takarda ce a wurin Bikin Ranar Yara Mata ta bana da Cibiyar Al’adu ta Birtaniya (British Council, Nigeria) ta shirya da aka gudanar a ranar 9 ga Satumba, 2015, a Kano.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50