Hasumiyyar Gobarau: Ginin da ya haura shekara 600 a Katsina

Hasumiyar Gobarau na daya daga cikin dogayen gine-ginen tarihi a Jihar Katsina, kuma an yi has ashen cewa an gina ta wajen shekaru sama da 600 da suka gabata. An gina hasumiyar da irin tsarin gine-ginen Mali.Tarihi ya tabbatar da cewa an gina ta ne domin bauta, kuma daga bisani hasumiyyar ta dauki gurbin tsare […]

Hasumiyyar Gobarau: Ginin da ya haura shekara 600 a Katsina
Hasumiyyar Gobarau: Ginin da ya haura shekara 600 a Katsina

Hasumiyar Gobarau na daya daga cikin dogayen gine-ginen tarihi a Jihar Katsina, kuma an yi has ashen cewa an gina ta wajen shekaru sama da 600 da suka gabata. An gina hasumiyar da irin tsarin gine-ginen Mali.
Tarihi ya tabbatar da cewa an gina ta ne domin bauta, kuma daga bisani hasumiyyar ta dauki gurbin tsare garin daga mahara, ta hanyar hango abokan gaba kafin su iso garin. A yau hasumiyar na daya daga cikin alamun ita kanta Katsina, wadda kan jawo mutane don yawon bude ido.
Hasumiyar ita ce masallacin Juma’a na farko a tsohon birnin Katsina, wanda aka gina tsakanin shekarar 1348 zuwa1398, sannan akwai kasuwa kusa da gefenta. Asalinta ta fi yadda take a yau tsawo. Wasu masana sun ce ta ninka yadda take a yanzu. Bugu da kari hasumiyar ta fadi, domin rashin kulawa, musaman a zamanin mulkin Sarkin Katsina Umarun Dallaje; domin a lokacin an fi mayar da hankali kan yada jihadi tare da koyarwa da tabbatar da adalci tsakanin mutane. Sai a zamanin Sarki Dikko aka kara gina ta, bayan ta zagwanye tare da yi wa hasumiyar kwaskwarima.
Bugu da kari, daga bisani da aka gina masallacin Juma’a watau masallacin dutse a kusa da kofar Soro, a karni na sha takwas sai aka karkata can, a yayin da malamai suka rika Salla a masallatan unguwanni ko a zaurukan da suke koyarwa. Haka ya kara rage yawan masu zuwa Gobarau.
Tarihi ya tabbatar da cewa masallacin Gobarau ya kafu ne kusan a lokacin da Musulunci ya zo Katsina, kamar yadda aka samu daga masanin tarihin nan, Sheikh Muhammadu Abdulkarim Almaghili, a bayanin Sarkin Katsina Musulmi na farko, wato Sarki Muhammadu Korau. Inda a lokacin da Almaghili ya kawo ziyara Katsina sai ya nemi a gina masallaci don bauta tare da makaranta don karatu, yayin da aka gina masallacin Gobarau sai ya kasance shi ne masallaci na farko a Katsina.
Makarantar masallacin Goba-rau ta shahara, inda dalibai ke zuwa daga nesa, kuma an sami manyan malamai kamar su Sheikh kadi Muhammad Al-Tazakhti, Sheikh Muhammad Abdulkarim Almaghili, Sheikh Umar Bin Akit, Sheikh Ahmed Bab Ali Timbuktu da Sheikh Akib Al-Ansumani. Sannan akan karanta Alkur’ani, Hadisi, Fikihu, Hisabi, Mandaki, Harshen Larabci, Tarihi, Sha’ir, Falsafa da sauransu. Makarantar sai da ta dauki matsayin jami’a, musamman domin an yaye manyan malamai, wasu har sun kai darajar waliyyai. Bugu da kari, ana zuwa daga ko’ina a kasar Hausa don neman ilimi a Katsina.
Cibiyar tarihi da ke kofa Uku a unguwar Rafukka, Katsina sun yi bayanin cewa hasumiyar ta tabbatar da alaka tsakanin Katsina da Daular Songhai. Kuma mutanen dauri sun yi imanin cewa duk wanda ya hau kan hasumiyar zai hango dakin Ka’aba. Kamar yadda aka ruwaito cewa wata gardama ta kaure tsakanin malamai sai Malam Jodoma ya nuna Ka’aba daga kan hasumiyar kuma kowa ya gani! Yayin da ko a yau wasu na tsoron hawa saman hasumiyyar.
An tabbatar da cewa masana na zuwa ziyarar hasumiyar daga cikin Najeriya da wajenta domin binciken tarihi da gani da ido, musamman auna tasirin maginan da suka gabata. Malamai da masana da dalibai daga kusa da nesa sun taho har daga kasashen Jamus, Ingila, Amurka, Argentina, Sudan, Moroko, Canada, Ghana da Kamaru da wasu kasashen don su gani da kansu.
Gwamnatin Tarayya ta dauki hakkin kula tare da kare kayan tarihi, wadanda suka hada da hasumiyar Gobarau, duk da haka Majalisar Sarkin Katsina na taka rawar gani wajen tafiyar da harkokin da suka shafi hasumiyyar. A zamanin Sarki Kabir Usman, an yi wa hasumiyar karin kwaskwarima.
A yau an gina makarantar firamare a gefen hasumiyar, makarantar da ta shahara da sunan Gobarau. An kara wa hasumiyar kwaskwarima a zamanin mulkin Barista Ibrahim Shehu Shema, Gwamnan Jihar Katsina.
Hasumiyar ta Gobarau na karkashin kulawar Sarkin Maginan Katsina, wanda da izininsa ne ake gyara ko yin kwaskwarimarta. Sannan mukullen hasumiyar na wajen Akulle Tukur, wanda yake bude kofarta ga duk wanda ya kawo ziyara.
Daure, manazarci kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya aiko sakon nan daga Katsina

Kamfanonin waya na shirin ƙara kuɗin kira da na data a 2025

Mutum 5 da suka yi tashe a shafukan sada zumunta a 2024

NAJERIYA A YAU: Abin da ya sa ake bikin ‘Boxing Day’ a ranar 26 ga Disamba

Ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a gidan mutuwa a Borno