Hatsabibiyar gobara ta cinye gidan wani malamin Jami’ar danfodiyo
Wata hatsabibiyar gobara da ta tashi har sau hudu a lokuta mabambanta ta cinye gidan Dokta Abudullahi Mu’azu Saulawa wani malami a Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato.Dokta Saulawa sanannen masanin tarihi ne da jami’ar ke alfahari da shi, kuma majiyarmu ta ce wutar ta fara tashi ne tun ranar Alhamis din makon jiya, inda […]
Wata hatsabibiyar gobara da ta tashi har sau hudu a lokuta mabambanta ta cinye gidan Dokta Abudullahi Mu’azu Saulawa wani malami a Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato.
Dokta Saulawa sanannen masanin tarihi ne da jami’ar ke alfahari da shi, kuma majiyarmu ta ce wutar ta fara tashi ne tun ranar Alhamis din makon jiya, inda ta rika tashi jefi-jefi har zuwa ranar Lahadin da ta gabata, kuma ta lashe gidan gaba daya.
“Wutar ta fara ne daga kan itacen dogonyaro da ke cikin gidana, tashinta ke da wuya muka samu muka kashe ta, sai ranar Asabar da safe wutar ta sake kamawa a kabet na yarana wurin da suke a jiye littafansu. Ta kama sau biyu a lokaci daban-daban, wato safe da maraice aka kashe ta. Kwatsam a ranar Lahadin da ta gabata dukkanmu mun fita ba kowa a gidan da safe sai aka kira ni a waya cewa wuta ta kama gidana kafin in karaso ta cinye gidan gaba daya,” inji Dokta Saulawa.
Dokta Abdullahi Saulawa ya ce ya yi asarar littattafansa da ya kwashe shekara 62 da wata yana ajiye da su. “Ba na sa ran sake mai da asarar da na yi domin wasu littattafan nawa an daina buga su wasu kuwa lokacin da na tafi Ingila da Amurka da Jamus da sauran kasashe na samo su. Wasu rubuce-rubucena ma yanzu ne nake tunanin yadda zan mayar da su littattafai, su ma sun kone ba wani abu da muka fitar da shi a wannan waki’ar,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Wannan wutar hatsabibiya ce da ke bibiyar mutanen Sakkwato domin wani makwabcina ya labarta min kusan sau 15 wutar na tashi a gidansa, domin har yanzu ban san musabbabin wutar da ta tashi a gidana ba, tunda ka ga dai ta itace mai rai wanda yake tsaye ta fara. Ta karshen kuma ba kowa a gidan, ba wutar lantarki a lokacin, hasali ma mun fahimci ta fara ne ta wurin wanke-wanken gidan. Allah dai Ya sauwaka aiki ne wannan daga Ubangiji.”