Hatsabibiyar wuta ta gallabi wani kauye a Sakkwato

A ranar Asabar da ta gabata ne al’ummar  kauyen Siddingo da ke cikin karamar Hukumar Kware a Jihar Sakkwato  suka tashi da mummunar gobara da ta cinye kusan gidajen nasu gaba daya ba su tsira da wadansu kayan bukatunsu ba.Da Aminiya ta ziyarci kauyen, ta gano cewa wutar ta kwashe mako guda tana ci, an […]

Hatsabibiyar wuta ta gallabi wani kauye a Sakkwato
Hatsabibiyar wuta ta gallabi wani kauye a Sakkwato

 Iccen da maciji yake kafin a kashe shi da kuma yadda wutar ta cinye wani bangare na kauyenA ranar Asabar da ta gabata ne al’ummar  kauyen Siddingo da ke cikin karamar Hukumar Kware a Jihar Sakkwato  suka tashi da mummunar gobara da ta cinye kusan gidajen nasu gaba daya ba su tsira da wadansu kayan bukatunsu ba.
Da Aminiya ta ziyarci kauyen, ta gano cewa wutar ta kwashe mako guda tana ci, an kasa kashe ta.Wani wanda ya nemi a sakaya sunansa da yake bayyana wa wakilinmu musabbabin lamarin ya ce, “Gaskiyar lamari akwai wani dadadden maciji a wannan kauye, tun kaka da kakanni yake zaune cikin wani kogon icce a wani bayan gida da kakanmu marigayi yake zaune, kafin rasuwarsa shi yake kula da macijin, inda yake ba shi madara da nonon shanu.
“A lokacin da ciwon ajali ya same shi, lallai ya fada wa jikokinsa da ’ya’yansa cewa kada wanda ya kuskura ya taba maciji nan bayan ransa. Abinka da kaddara, sai wani daga cikin jikokinsa da ake kira danfulani ya je ya yi shaye-shayensa ya dawo ranar Jumu’a da ya ga macijin nan a fili ya kashe shi. Mutanen gari duka babu wanda ya ji dadin faruwar lamarin, sai aka haka rami aka turbude gawar macijin nan. Safiyar Asabar muka fada wannan masifar ta gobara, wadda muke ganin kashe macijin nan ce ta haddasa mana ita. Har iccen da macijin ke kwanciya ya kone, bayan gidajenmu sun toye.’’
Da wakilinmu ya tuntubi mutumin da wutar ta fara tashi a gidansa, watau Malam Aliyu Shehu, cewa ya yi shi kam bai san mafarin wutar ba, kawai gani ya yi wutar ta tashi a bukkarsa gaba daya gidansa ya kone, amma shi bai san mafarin gobarar ba.
Malam Aliyu ya kara da cewa, “Na ji ana yada jita-jitar cewa wai maciji aka kashe, shi ya kawo wannan, to ba gaskiya ba ne, don na san muna da wadansu macizai a wani kogon ice, wadansu na fadar biyu ne ko uku, an tabbatar mini cewa a lokacin da wuta ta kama gidan da ke kusa da iccen da suke ciki sun fita suka yi yamma da gari su biyu, fari da baki, bayan nan ne iccensu ya kama, shi ma ya kone.”
Ya cigaba da cewa, “Muna zargin akwai sa hannun iskoki a cikinsa, domin idan ka dubi yadda lamarin yake faruwa, misali a duk lokacin da wutar ta kama aka kashe ta, sai ta koma wani bangare na garin ta tashi, kuma a yini takan tashi sau uku ko hudu, tun lokacin da ta fara har zuwa yau, fiye da kwana goma da suka wuce, ta cinye mana damman gero fiye da 300 da rufewa tara da dakuna sama da 20 da kayan dakunanmu. Kamar dai yadda kake gani, yanzu mun bar garin gaba daya mun koma gefen garin kafin lamarin ya kwanta mu dawo, ba a samu salwantar rayuka ba.”
Magaji Umaru  shi ne Hakimin Siddingo da yake zantawa da wakilinmu ya ce shi bai san mafarin wanan gobarar da ba su taba ganin irinta ba.Ya ce, “Wannan wutar ga dukkan alamu tana dauke da iska (Jinnu), domin duk abin da aka dauka daga garin aka kai shi wani kauye sai wutar ta je ta cinye shi. Jiyan nan (Lahadi), aka dauki kara masu yawa aka kai kauyen ’Yar Kanta, amma sai da wutar nan ta same su ta cinye duka. Don haka yanzu komai ba a dauka daga nan zuwa wani wuri domin gudun kada a kai musu musiba”.
A karshe, ya yi kira ga karamar |Hukumar Kware ta kawo musu dauki, “Don ko jiya (Lahadi), cikin bukka tara da mutane suka yi don samar wa yara da mata mafaka wutar ta zo ta cinye guda shida”. Inji shi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa mutanen garin suna cikin juyayi da fargaba da tsoro, saboda ba su da wata mafita don kawo karshen wannan wutar da ke bibiyarsu  fiye da kwana goma, domin  ko a gabansa ma sai da wutar ta tashi a wata bukka, aka kashe ta. Mutanen garin sun bayyana masa cewa, haka wutar take tashi jefi-jefi ana kashe ta.
Alhaji Shehu Zamau, shi ne shugaban karamar Hukumar Kware, duk kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakinsa kan shirin da suke yi ga al’ummar Siddingo, abin ya ci tura.