Hatsaniyar rufe layukan waya

An samu hatsaniyar a ofishoshin kamfanonin waya a sassan kasar nan a lokacin da msu amfani da wayoyin suka garzaya don bude layukan wayoyinsu da kamfanonin wayar suka rufe, sakamakon umarni daga Hukumar Kula da Sadarwa ta kasa (NCC) ta ba dukkan kamfanonin wayar su fara rufe layukan da aka yi musu rajista kafin sayar […]

Hatsaniyar rufe layukan waya
Hatsaniyar rufe layukan waya

An samu hatsaniyar a ofishoshin kamfanonin waya a sassan kasar nan a lokacin da msu amfani da wayoyin suka garzaya don bude layukan wayoyinsu da kamfanonin wayar suka rufe, sakamakon umarni daga Hukumar Kula da Sadarwa ta kasa (NCC) ta ba dukkan kamfanonin wayar su fara rufe layukan da aka yi musu rajista kafin sayar da su ko wadanda ba a cika ka’ida wajen yi musu rajista ba, tare da ba su mako daya su yi haka ko su fuskanci fushin hukumar a watan jiya.
Umarnin ya biyo bayan ganawa a tsakanin ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro (NSA) da Hukumar Tsaron kasa (DSS) da kamfanonin wayoyin lantarki da Hukumar NCC.
Ganawar ta duba irin miyagin ayyuka da ake yi ga jama’a ya alla masu satar mutane da ’yan ta’adda da ’yan fashi da makami da masu barazana ga rayuka ta hanyar amfani da layukan waya marasa rajista da suka shafi dukkan kamfanonin.
Dukar Hukumar NCC ta 19 (1) da 20 (1) ta yin rajistar masu amfanin da layukan waya ta tanadi tarar Naira dubu 200 ga duk wani layin waya da aka yi rajistarsa kafin sayar da shi ko rashin yin cikakkiyar rajistar layin wayar ko yin rajistar ba daidai ba, matukar aka aiske ana amfani da ita a layin kamfanin sadarwa.
Rajistar layukan waya da aka gudanar shekara biyu da suka gabata, an yi ne domin a san dukkan masu amfani da layukan waya, sai dai kuma wasu kamfanonin wayar sun rika yin rajistar layukan sannan aka rika sayar wa jama’a, yin hakan ya ruguza manufar shirin, muhimmi daga ciki a yaki miyagun laifuffuka.
Sai ya zamo suna bari ana keta dokoki matukar bukatarsu ta samun karin abokan hulda za ta biya. Idan ba haka ba, ba za a samu miliyoyin layukan wayoyin da ba a yi musu rajista ba.
A cewar Hukumar NCC, kimanin layukan tarho miliyan 38 da dubu 780 ne aka gano rajistarsu ba ta cika ba a dukkan kamfanonin, inda miliyan 10 da dubu 700 aka rufe su.
Tashin hankalin ya biyo bayan wannan mataki da Hukumar NCC ta dauka kan kamfanonin wayar ya faru ne sakamakon yadda hukumar take rikon sakainar kashi wajen sanya ido ga kamfanonin, domin inda ta dauki matakai masu gauni ba za su yi abin da suka ga dama ba.
Kuma kamar yadda aka saba, masu amfani da layukan wayoyin ne gazawar Hukumar NCC da kamfanonin sadarwar za ta cutar, domin hatta wadanda suka rajistar babu wanda ya shaida musu akwai abubuwan da aka yi ba bisa ka’ida a tsawon wannan lokaci, ba a sanar da su cewa ba su yi rajista ba ko su je su yi rajista yadda ya kamata.
Kuma wasu da aka tura wa sakon ba su da matsala a rajistar layukansu, amma kamfanonin wayar suka rika tura wa kowa sakon ciki har da wadanda abin bai shafa ba. Wannan abu ya fusata mutane da dama, kamata ya yi su bincika su ciro sunayen wadanda suke da matsala da rajistarsu kawai su aika musu sakonnin su kadai. Duk wannan na nuna yadda ba a tafiyar da al’amura daidai, kuma Allah ne kawai Ya san miyagu nawa ne za su ci gajiyar wannan gazawa ta samun rajistar layukan waya ba tare da yin rajista yadda ta kamata ba, ko ma ba tare da yin rajistar ba kacokan, inda hakan zai sanya rayuka da dukiyar jama’ar kasa a cikin hadari. An rika kama wasu daga cikin ’yan ta’adda da masu satar mutane da layukan waya masu yawa inda suke yin amfani da su sai su cire don aikata miyagun ayyukansu. Ba za ka iya gano wadannan miyagu mutane ne, sakamakon sakacin kamfanonin sadarwa.
Ko ma mene ne, masu amfani da layukan suna da wata yarjejeniya da kamfanonin sadarwar kuma wajibi ne su samu ingantaccen aiki da kula mai kyau ba a rika yi musu yadda aka ga dam aba.
Hukumar NCC a wani gefen ta hannun Mataimakin Shugabanta da Babbar Jami’ar Zartarwarta Efosa Idehen da Yetunde Akinloye ta ba kamfanonin sadarwar da ke Najeriya zuwa 9 ga Satumban nan kan su biya tarar Naira miliyan 120 da dubu 400 saboda gazawarsu na su yi aiki da umarnin rufe layukan da aka yi musu rajista kafin sayar da su da kuma rufe layukan kwata-kwata daga hanyoyin sadarwarsu.  
Muna fata wannan gyaran rajistar layukan wayoyin ta zamo na karshe, domin mutane sun gaji da yadda ake wahalar da su wajen tantancewar na’urori da wasu hukumomi ke yi, amma a ce sai sun sake yi a wasu wuraren. Muna bukatar a samar da hanyar da za a rika adana bayanai ta yadda zai amfani sauran hukumomin da suke bukatar bayanan, don haka muna maraba da jin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kwanan nan ya ba da umarnin a daidaita bayanai kan jama’a tare da adana su a kasar nan.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50