Hatsari: Ganduje ya yi alhini kan mutum 17 da suka rasu a Kano

Mutuwar tasu ta zo mana da matukar girgiza, kuma wannan ba karamar asara ba ce.

Hatsari: Ganduje ya yi alhini kan mutum 17 da suka rasu a Kano

Yadda aka yi jana’izar wasu daga cikin mamatan a Unguwar Sani Mainagge

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya jajanta wa iyalan mutum 17 duka maza da suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su ranar Asabar a kan babban hanyar Kano zuwa Zariya.

Ganduje ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan cikin wata sanarwa  da Sakataren Sadarwa na Fadar Gwamnatin Kano, Alhaji Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi.

“Mutuwar tasu ta zo mana da matukar girgiza, kuma wannan ba karamar asara ba ce ga ’yan uwansu ko kuma mutanen Unguwar Sani Mainagge da ke Karamar Hukumar Gwale inda suka fito.

“Mutuwarsu babban rashi ne ga gwamnati da kuma al’ummar Jihar Kano baki daya wanda wannan lamari ne da ya zo daga Allah kuma Shi kadai ne zai iya gafarta musu.

“Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya sa Aljannah ce makomarsu kuma Ya yafe musu kurakuransu tare da bai wa ’yan uwansu hakurin jure wannan babban rashi da aka yi,” a cewar Ganduje.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewar, a madadin gwamnati da jama’ar Kano, Ganduje ya janjanta wa iyalai, mutanen Unguwar Sani Mainagge, abokansu da kuma dukkanin danginsu kan wannan abin bakin ciki.