Hatsarin ayarin Mataimakin Gwamnan Sakkwato ya kashe ’yan tawagarsa
Motar jami’an tsaro a tawagar mataikin gwamnan ta yi adungure a lokacin da suke hanyar zuwa mahaifar mataimakin gwamnan.
![Hatsarin ayarin Mataimakin Gwamnan Sakkwato ya kashe ’yan tawagarsa Hatsarin ayarin Mataimakin Gwamnan Sakkwato ya kashe ’yan tawagarsa](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2022/02/Hatsari-Hoto-daga-Bloomberg.jpg)
Hoton wani hatsarin mota. (Hoto: Bloomberg)
Hatsari ya ritsa da ayarin motocin Mataimakin Gwamna Sakkwato, Idris Gobir, inda hakan ya ’yi ajalin wani dan sanda da wani mai daukar hoto a tawagar.
Mutanen biyu sun gamu da ajalinsu a wannan hatsari ne bayan wata motar jami’an tsaro a cikin tawagar mataimakin gwamnan ta kwacce sannnan ta yi adungure a yankin Yanrimawa da ke kan hanyar Goronyo-Sabon Birni
Hatsarin ya auke ne a lokacin da mataimakin gwamnan da ayarin nasa suke kan hanyarsu ta zuwa mahaifarsa, Sabon Birni a ranar Laraba.
Injiniya Idris ya tafi kauyen nasu ne domin kabar bakuncin Gwamna Ahmed Aliyu da zai kai ziyarar ta’aziyya a yankin.
- Hisbah ta kama mota maƙare da kwalaben barasa dubu 24 a Kano
- An kama likitar bogi kan zargin kashe mai juna biyu a Kano
Darakktan yadaa labaran mataimakin gwamnan, a tabbatar da rasuwar dan sandan da ke tuka motar da kuma wani mai daukar hoto da ke ciki motar.
A cewarsa an kai gawarwakin dakin ajiyar gawa.