Hatsarin DAF da bas ya kashe mutane 14 a Jigawa

Wani hatsarin mota ya lakume rayukan mutane 14 a kan babbar hanyar Kanya a Jihar Jigawa.

Hatsarin DAF da bas ya kashe mutane 14 a Jigawa

Tirelar raken da ta yi hatsari a Babbar Hanyar Kubwa da ke Abuja

Wani hatsarin mota ya lakume rayukan mutane 14 a kan babbar hanyar Kanya a Jihar Jigawa.

Wasu mutane hudu na asibiti a sakamakon hatsarin na ranar Talata tsakanin wata tirela kirar DAF da wata bas kirar Toyota Hiace.

Motocin biyu sun yi karo ne gaba-da-gaba a kusa da wani shingen binciken babban hawa na jami’an hukumar shige da fice.

Ganau sun bayyana cewa Hiace din da ke mugun gudu ce ta yi kokarin wuce wata mota, wanda hakan ya yi sanadin karonta da DAF din.

Jami’an lafiya a asibitin Kanya Babba Cottage sun tabbatar da adadin mamatan da kuma wadanda suka ji rauni a sakamakon hatsarin.

Kakakin ’yan sand ana Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce rundunar ta fara bincike kan lamarin, musamman kan zargin mugun gudun bas din.