Hatsarin kwalekwale ya yi ajalin mutum 10 a Neja

Daga cikin mutanen da suku mutu, 9 mata ne, 1 namiji

Hatsarin kwalekwale ya yi ajalin mutum 10 a Neja

Kifewar kwale-kwale

Akalla mutum 10 ne rahotanni suka tabbatar da mutuwarsu sakamakon kifewar kwalekwale da yammacin Alhamis a Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 4:00 na yammacin Alhamis.

Hatsarin dai ya ritsa da mutanen ne, wadanda galibinsu ’yan kasuwa ne da ke kokarin kai kaya daga kauyen Zongoru na gundumar Bass, a kan hanyarsu ta zuwa Gijiwa, domin shirin cin kasuwar Kuta, hedkwatar Karamar Hukumar Shiroro da ke Jihar.

Bayanai sun ce mutum 32 ne a cikin jirgin lokacin da ya kife, inda mutum 10 suka mutu, 22 kuma masunta suka ceto su da ransu.

Saidu Salihu, Sakataren kungiyar ci gaban Shiriro, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Aminiya, inda ya ce tara daga cikin wadanda suka rasu tara mata ne, daya kuma namiji.

Sai dai duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.