Hatsarin kwalekwalen Taraba: An gano gawarwaki 17, an ceto 12

Hukumar ta ce tana ci gaba da gudanar da aikin ceto.

Hatsarin kwalekwalen Taraba: An gano gawarwaki 17, an ceto 12

Hukumar Bayar da da Agajin Gaggawa (NEMA) ta ce jami’an ceto sun gano gawar mutum 17 bayan da wani jirgin ruwa dauke da mutane 104 ya kife a Jihar Taraba.

Kazalika, hukumar ta ce ta freeceto mutum 12.

Jirgin ruwan ya kife ne a ranar Asabar da ta gabata, inda sama da mutum 100 wanda galibinsu ’yan kasuwa ne da suka hada da mata da kananan yara da ke dawowa daga kasuwar kifi ta Mayorenero da ke Karamar Hukumar Ardo – Kola a kan hanyarsu ta zuwa Binnari da ke Karamar Hukumar Lamido duk a Jihar Taraba.

Daraktan NEMA, Bashir Garga, ya ce ana ci gaba da aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

Jirgin ruwan ya kife ne a kogin Benuwe.

An birne wasu daga cikin wadanda suka rasu a bakin kogi a Mayoreneyo da Binnari.

Shugaban riko na masu jigilar ruwa a Taraba, Jidda Mayoreneyo, ya shaida wa Aminiya cewa an yi jana’izar shida daga cikin wadanda suka mutu a jiya a garin Mayoreyo.

Ya ce iyalan wadanda abin ya shafa sun bai wa kungiyar izinin birne su.

Ya kara da cewa an birne sauran wadanda abin ya shafa a Binnari inda kwale-kwalen ya kife a ranar Asabar.

Jidda ya kara da cewa an birne wasu hudu da aka gano a bakin kogi bayan amincewar iyalansu.

Wani mazaunin garin Saidu Audu, ya ce jirgin ya taso ne daga Mayorenyo dauke da mutane da yawa da kuma kaya masu nauyi.

“Baya ga mutanen da ke cikin jirgin, akwai sabbin babura, buhunan siminti, damin rake, da sauran kayayyaki,” in ji shi.

Wani mazaunin garin Dauda ya shaida wa Aminiya cewa masu jiragen ruwa a wasu lokuta kan yi lodi fiye da kima, kuma babu wata hukumar gwamnati da za ta tsara yadda ya kamata su gudanar da ayyukansu.

Yana da wuya a iya ba da hakikanin adadin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka kubuta kawo yanzu.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota