Hatsarin mota ya ci rayukan mutum 21 a Enugu

Hukumar Kiyaye Hadura ta kasa (FRCS) ta tabbatar da rasuwar mutum 21 cikinsu har da dalibai, a wani  hatsarin mota da ya auku a yankin Mgbowo da ke Karamar Hukumar Awgu ta jihar Enugu. Kwamandan FRSC na jihar, Ogbonna Kalu, ya shaidawa jaridar Punch ta wayar tarho, cewar lamarin ya faru ne a ranar Laraba. […]

Hatsarin mota ya ci rayukan mutum 21 a Enugu

Hukumar Kiyaye Hadura ta kasa (FRCS) ta tabbatar da rasuwar mutum 21 cikinsu har da dalibai, a wani  hatsarin mota da ya auku a yankin Mgbowo da ke Karamar Hukumar Awgu ta jihar Enugu.

Kwamandan FRSC na jihar, Ogbonna Kalu, ya shaidawa jaridar Punch ta wayar tarho, cewar lamarin ya faru ne a ranar Laraba.

“An rasa rayuka 21 ciki har da wasu dalibai da motar makaranta ke dauke da fiye da dalibai 50.

“Amma daga cikin wanda suka mutu, akwai masu tafiya a gefen hanya”, cewar Kalu.

Ya bayyana cewa bayan bincike sun gano cewar tukin ganganci ne ya haifar da hatsarin inda wata tirela a kan babban titin Awgu ta kwace kuma murkushe motar makarantar da ke dauke da dalibai sama da 50 a cikinta.

Bayan tabbatar da rasuwar mutane 21 an samu wanda suka ji rauni da dama.

Wani ganau ya ce direban motar ya tsere cikin daji ganin irin ta’asar da ya tafka.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa