Hatsarin mota ya hallaka mutum 12 a hanyar Kano zuwa Katsina
Mutum shida ciki har da direban motar sun mutu nan take, yayin da wasu shida suka rasu bayan an garzaya da su asibiti.
Taswirar Jihar Katsina
Aƙalla mutum 12 ne suka rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a yankin Gidan Mutum Daya da ke kan hanyar Kano zuwa Katsina.
Rahotanni sun ce hatsarin ya rutsa da wata tirela da kuma motar haya ta Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA), inda motocin biyu suka yi taho-mu-gama da juna da misalin karfe 8:30 na dare a ranar Lahadi.
- Za a rataye matasa 2 saboda kashe abokinsu a dalilin cacar baki kan ƙwallon ƙafa
- Ɗan Abacha ya gaza samun tikitin takarar Gwamnan Kano a PDP
Aminiya ta ruwaito cewa mutum shida ciki har da direban motar sun mutu nan take, yayin da wasu shida suka rasu bayan an garzaya da su asibiti sakamakon munanan raunukan da suka samu.
Haka kuma, mutum biyu na ci gaba da karɓar magani a Babban Asibitin Katsina, yayin da aka sallami wasu biyar bayan duba lafiyarsu.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana alhininsa kan lamarin, yana mai cewa jihar ta yi babban rashi.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jiƙan mamatan Ya kuma bai wa iyalansu haƙurin jure wannan ibtila’i.
Kazalika, gwamnan ya buƙaci direbobi da su riƙa kiyaye dokokin hanya domin kauce wa irin wannan tsautsayi.