Hatsarin mota ya kashe mutum 12 a Zamfara
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa FRSC ta alakanta aukuwar hatsarin da tukin ganganci.
Akalla mutum 12 ne ajali ya katsewa hanzari ciki har da yara biyu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
Lamarin, kamar yadda wani ganau ya shaida wa wakilinmu, ya ce ya faru ne da misalin ƙarfe 1:20 na rana a kan babbar hanyar Funtuwa zuwa Tsafe.
- Harin ’yan ta’adda ya yi ajalin mutum 16 a Yobe
- CBN ya musanta yunƙurin ƙirƙirar sabbin takardun Naira a baɗi
Wakilinmu ya ruwaito cewa, hatsarin ya rutsa da mutum 24 — 22 a cikin wata motar haya da wasu mutum biyu a wata A Kori Kura kirar Toyota.
Hatsarin wanda ya auku a sakamakon tsautsayi, bayanai sun ce an yi taho-mu-gama ne tsakanin motocin yayin da gudanarwar motar hayar ta kwace daga hannun direbanta.
Yanzu haka dai an kwantar da wadanda suka jikkata a Babban Asibitin Tsafe, inda suke karɓar magani.
Wani jami’in Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) da ya bukaci a sakaya sunansa, ya alakanta aukuwar hatsarin da tukin ganganci.
“Ina cikin jami’an FRSC da suka kai dauki wurin da hatsarin ya faru wanda ya rusta da mutum 24 a duk motocin biyu.
“Wadanda suka mutu sun hada wasu mutum 10 da kananan yara biyu, yayin da kuma da dama suka jikkata,” a cewarsa.