‘Hatsarin mota ya lakume rayuka 84 cikin wata 11 a Gombe’
Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ce ta tabbatar da hakan a Gombe.
Kimanin mutane 84 ne suka mutu a hatsarin mota 350, wasu 939 kuma suka samu munanan raunuka daga watan Janairu zuwa Nuwamban shekarar 2021 a Jihar Gombe.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar, Ishaku Gabmi Ibrahim, ne ya bayyana hakan a kididddigar rahoton hukumar da ya fitar ranar Alhamis.
- DPO ya lashe musabakar Alkur’anin ’yan sanda ta farko a Kano
- Sanya takunkumi ya fi rigakafi zama kariya daga COVID-19 – Sabon bincike
A cewarsa haduran sun ritsa da fasinjoji 1,548 ne, a cikinsu 525 kuma suka tsira ba su samu rauni ba.
Kwamandan ya ce daga watan Janairu zuwa Maris, an samu aukuwar hadura guda 102, inda mutum 32 suka mutu, wasu 298 kuma suka ji rauni.
Kazalika, ya ce a tsakanin watan Afirilu da Yuni, an samu mutuwar mutum 32, wasu 319 suka ji rauni, sannan wasu 16 ma suka mutu 269 suka samu raunuka a tsakanin watan Yuli zuwa watan Satumba.
Ishaku, ya kuma ce a tsakanin watan Oktoba zuwa Nuwamba kuwa, an samu mutum hudu da suka mutu 53 suka ji rauni a wasu hadura 22 daban-daban da suka faru.
Daga nan sai Kwamandan ya roki direbobi da sauran masu amfani da hanyoyi da su zama jakadun hanya na gari wajen bin dokokinta domin gujewa asarar rayuka ta dalilin faruwar haduran.