Hatsarin mota ya lakume rayukan fasinjoji 12 a Yobe

Aƙalla fasinjoji 12 ne da suka haɗa da maza 10, mata biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon  wani hatsarin mota da ya auki a kan titin Baimari zuwa Geidam a Jihar Yobe.

Hatsarin mota ya lakume rayukan fasinjoji 12 a Yobe

Aƙalla fasinjoji 12 ne da suka haɗa da maza 10, mata biyu suka rasa rayukansu sakamakon  wani hatsarin mota da ya auku a kan titin Baimari zuwa Geidam a Jihar Yobe.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗura (FRSC), reshen Jihar Yobe,  Corps Livinus Yilzoom ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Damaturu.

A cewarsa, hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ƙauyen Chelluri da ke kan titin na Baimari zuwa Geidam.

Ya kuma bayyana cewa hatsarin ya rutsa da wata babbar mota ƙirar Howo mai lamba MAG831ZR mallakin kamfanin Dan Nene Construction da wata ƙaramar mota Bas ƙirar Sharon mai lamba, BAU124YF.

Ƙaramar motar ta shiga ƙarƙashin babbar motar wadda nan take ta kama wuta, kuma take kone fasinjojin motar 12 suka ƙone ƙurmus.

Ya ce binciken ya nuna cewa babbar motar ta ce ta kawo cikas a kan hanyar, yayin da direban Sharon ɗin ya gaza kauce wa motar.

Sai dai ya gargaɗi masu ababen hawa da su guji tafiye-tafiye cikin dare saboda hatsarin rashin ganin abin da ke kan hanya.

Har ila yau, ya yi gargaɗi direbobi da su guji yin tafiyar dare a lokutan hunturu da ake yawan samun hazo

Ya kuma yi kira ga masu ababen hawa da su riƙa bin ƙa’idojin hanya.